UNDP ta koyar da matasa sana’o’i a Adamawa

Hukumar Raya kasashe ta Majalisar dinkin Duniya (UNDP) ta koyar da matasa 50 sana’o’in hannu domin samun rufin asiri wajen gudanar da harkokin rayuwarsu a Jihar Adamawa.  Shugaban Hukumar UNDP a jihar, Dokta Samuel Bwalya ya ce sun gudanar da shirin ne domin domin taimaka wa matasan Najeriya  da kara musu kwarin gwiwa don ci […]

UNDP ta koyar da matasa sana’o’i a Adamawa


Hukumar Raya kasashe ta Majalisar dinkin Duniya (UNDP) ta koyar da matasa 50 sana’o’in hannu domin samun rufin asiri wajen gudanar da harkokin rayuwarsu a Jihar Adamawa. 

Shugaban Hukumar UNDP a jihar, Dokta Samuel Bwalya ya ce sun gudanar da shirin ne domin domin taimaka wa matasan Najeriya  da kara musu kwarin gwiwa don ci gaban kasa kamar yadda Shugaban Ayyuka na Hukumar UNDP, Mista Robert Asugwa ya bayyana.

Mista Asugwa ya ce suna iya kokarinsu don ganin cewa an hadasu da Gwamnatin Tarayya domin gani da kuma sanin irin hanyoyin da za a bi wajen taimaka wa matasa.                                                 

Ya kara da cewa “Domin samun ci gaba, muna bukatar matasan da suka jajirce wajen sana’o’in hannu, wannan shi ne dalilin hada irin wannan shiri da muke yi,” inji shi.

Kuma ya yi kira ga matasan su dage wajen kwarewa a fanonin sana’o’insu domin samun ci gaban kasa.

“Za mu rika kai musu ziyara domin ganin irin kalubalen da suke fuskanta,” inji shi.   

Shi ma Shugaban Hukumar Kula Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa (SEMA), Alhaji Haruna Furo ya nuna farin cikinsa kan yadda UNDP ta taimaka wa matasan.

Furo ya bukaci matasan su yi amfani da ilimin da suka koya domin yi wa kai amfani da rage matasa masu zaman banza a gari banza.