UNESCO ta sanya hawan Dabar Kano cikin kundinta na Al’adun Duniya
Hukumar al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta sanya bukukuwan hawan Sallar Idin da ake yi a Kano cikin manyan al’adun duniya masu ɗimbin tarihi.
Hukumar kula da al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta sanya bukukuwan hawan Sallar Idin da ake yi a birnin Kano da ke yankin arewacin Najeriya cikin manyan al’adun duniya masu ɗimbin tarihi.
Bikin da ake gudanar da shi tun daga ƙarni na 15 ya haɗa da yadda Sarki ke jagorancin tawagar da ta ƙunshi hakimai da fadawa da kuma mahaya dawaki sama da 10,000 waɗanda suka ci ado ana kuma buga musu tambura da busa algaita akan wasu titunan birnin.
Waɗannan bukuwan dai ana yinsu ne sau biyu a shekara, wato bikin ƙaramar Sallah ko Eid el Fitr da babbar Sallah ko kuma Eid el Adha, a watan 10 na Shawwal da kuma Zul Hajj wato watan 12 na Islama.
Bikin da ake kira Hawan Daba na kuma gudana a birane da dama na Musulmi a ƙasar da Hausawa suka fi yawa a yankin arewacin ƙasar, sai dai hukumar UNESCO ta ce sun samo assali ne daga birnin Kano, birni na 2 mafi girma a Najeriya mai dauke da mutane sama da miliyan 4 a cikin ƙwaryarsa, kuma birni na 2 na shugaban addinin Islama mafi girma a ƙasar.
Hajo Sani wadda ke wakilatar Najeriya a Hukumar UNESCO, ta bayyana bikin Hawan Dabar a matsayin wadda ke nuna irin addo da mutunci da kuma haɗin kan dake tsakanin al’umma mazauna birnin.
Ta ƙara da cewar bikin na da matuƙar girman da ke janyo ƙabilu daban daban domin gabatar da al’adun su ciki harda Hausawa da Fulani da Larabawa da Nufawa da Yarbawa da kuma Abzinawa waɗanda da dama daga cikinsu sun rikiɗe sun zama al’umma guda a birnin.
Sarkin Kano ke jagorancin bukukuwan tare da rakiyar hakimai da dagatai da fadawa waɗanda ke cin ado na fitar hankali domin bayyana irin farin cikin da suke ciki.
Sarkin kan ratsa wasu titunan birnin, yayin da jama’ar gari suna fitowa bakin titi suna miƙa gaisuwarsu tare da jinjinawa shugaban.
Sarakuna a halin yanzu basu da ƙarfin iko a ɓangaren gwamnati, amma kuma suna da ƙarfin faɗa aji a tsakanin al’ummominsu waɗanda suka mayar da su a matsayin masu killace al’adu, abinda ke basu ƙarfin faɗa aji a tsakanin al’umma.
Hawan Dabar na kuma taimakawa wajen samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa al’ummomi saboda rawar da suke takawa ta fuskar shirya bukukuwan.
A wannan shekara ‘Yan sandan Kano sun hana hawan Sallar saboda rikicin Masarautar Kano da aka samu.
Baya ga Hawan Dabar, bikin al’adar Sukur da ake yi a kusa da iyakar Kamaru da kuma bikin al’adar mutanen Osogbo dake Jihar Osun suma sun samu shiga cikin jerin bukukuwan na UNESCO.