Ungozoma ta yi kyautar jariri ba tare da sanin mahaifiyarsa ba
Wata da ke aikin ungozoma tare da ba da magungunan gargajiya a gidanta da ke garin Zuba a yankin Birnin Tarayya, Abuja mai suna Madam Elizabeth Oyeleke na fuskantar zargin aikata laifin raba jariri da mahaifiyarsa, ta hanyar kyautar da shi ga wata mai gidan kula da yara mai suna Misis Olufemi E. O, a […]
Wata da ke aikin ungozoma tare da ba da magungunan gargajiya a gidanta da ke garin Zuba a yankin Birnin Tarayya, Abuja mai suna Madam Elizabeth Oyeleke na fuskantar zargin aikata laifin raba jariri da mahaifiyarsa, ta hanyar kyautar da shi ga wata mai gidan kula da yara mai suna Misis Olufemi E. O, a daidai lokacin da uwar jaririn ke fama da kanta bayan ta haife shi a gabanta.
Uwar jaririn wadda budurwa ce da ta haife shi ba tare da yin aure ba mai suna Ebere Madu, ta shaida wa babban ofishin ’yan sanda na yankin Suleja, inda ta kai korafin cewa, matar wadda ta je wajenta don ta taimaka mata ta haihu, da farko ta shaida mata cewa tana bukatar hutu da kuma karin lafiya kafin a nuna mata abin da ta haifa.
Ta ce bayan tsawon lokaci ba tare da ba ta jaririn ba, sai ta sanar da wata ’yar uwarta al’amarin ta waya duk da cewa ba ta san tana da ciki ba, inda suka sanar da ’yan sanda al’amarin.
’Yan sanda sun kama ungozomar da kuma matar wadda ta yi ikirarin tana da gidan kula da yara a yankin Birnin Tarayya, Abuja, kafin ta dawo da jaririn wanda a yanzu haka ake kula da shi a sashin walwalar jama’a na gwamnati da ke Suleja.
Sai dai a bayaninsu bayan an kama su, ungozomar ta shaida wa ’yan sanda cewa uwar jaririn ce ta zo gare ta, inda ta sanar da ita cewa tana bukatar a zubar mata da ciki, wanda a lokacin ya kai wata takwas.
“Na shaida mata cewa ni ba na zubar da ciki in ban da kula da haihuwa da nake yi, sai kuma ba da maganin gargajiya,” inji ungozomar.
Ta ce, ta kuma shaida mata cewa zubar da ciki a wannan lokaci na iya barazana ga ranta. Haka nan ta ce bayan yarinyar ta gaya mata cewa ba ta bukatar abin da za ta haifa, kasancewar magabatanta ba su san tana da ciki ba, ta sanar da ita cewa akwai wajen kula da yara da za su dauki abin da ta haifa, kuma abin da ta yi ke nan bayan haihuwar.
Ita ma mai wajen kula da yaran ta musanta sayen jaririn. Ta ce ta dauke shi ne bisa hali na jinkai. Sauran wadanda ’yan sandan suka gayyata don ba da bayani a kan al’amarin, sun hada da uban jaririn wanda dan kasuwa ne a babbar kasuwar Suleja, mai suna Uche Osueka, wanda ya ce bai san da lokacin da ta haihu ba, sai kuma ’yar uwar mahaifiyar jaririn da kuma wata mace da aka ce ta taka rawa a wajen sada uwar jaririn zuwa wajen ungozomar.
Babban jami’in ’yan sanda mai kula da shiyyar Suleja, ACP Abubakar Yahaya ya tabbatar da faruwar al’amarin. Ya ce an ba da belin wadanda ake zargin, kuma za a maida batun zuwa rundunar ’yan sanda ta Abuja kasancewar inda lamarin ya faru yankin Zuba ne da ke Abuja, ba Madalla ba, da ke Jihar Neja.