UNICEF ta tallafa wa Kano da kayan adana alluran rigakafi

UNICEF ta ce ta bayar da tallafin ne domin samun damar adana alluran rigakafi a jihar.

UNICEF ta tallafa wa Kano da kayan adana alluran rigakafi

Asusun Tallafa wa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), ya tallafa wa asibitocin Jihar Kano da kayayyakin sanyi don adana alluran rigakafi wanda zai kare su daga saurin lalacewa.

Kayayyakin da UNICEF ta bayar sun haɗa da akwatunan sanyi guda 39 da abun zuba allurain rigakafi guda 1420 da katan-katan na sanya kankara mai nauyin 0.6 da kuma wasu katan-katan na sanya kankara mai girman 0.3 guda 1704.

A yayin raba kayayyakin Shugabar UNICEF, Rahama Rigood Mohammed Farah, ta bayyana cewa sun bayar da kayayyaki ne, domin ganin duk alluran da ake amfani da su wajen rigakafi sun ci gaba da zama a yanayin da ake so har zuwa lokacin da za a bai wa yara ba tare da sun lalace ba.

A cewar Rahama za a raba kayayyakin ne ga asibitocin da ke mazabu 484 a ƙananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.

“Wannan kayayyakin za su taimaka wajen adana alluran rigakafi. Za mu iya rarraba alluran rigakafi a duk loko da sakunan da ke jihar nan ba tare da wata matsala ba.”

Ta ƙara da cewar kayayyakin sun zo a lokacin da ya dace duba da cewar a kwanan nan suna shirin gudanar da gangamin yaki da cutar shan-inna, inda za su yi rigakafi ga ƙananan yara, kamar yadda suka saba.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7