Unileber ya zuba jarin Naira miliyan 90 don daliban sakandare

Kamfanin Unileber Nigeria ya kaddamar da gasar zane-zane don fito da hazakar daliban makarantar sakandare. Shirin wanda aka yi wa lakabi da ‘Unleash Your Potential’ an kaddamar da shi ne a ranar Juma’a a Legas, kamfanin ya ware miliyan 90 don gudanar da shi, inda daliban da suka samu nasara za su samu kyautar Naira […]

Unileber ya zuba jarin Naira miliyan 90 don daliban sakandare
Unileber ya zuba jarin Naira miliyan 90 don daliban sakandare

Kamfanin Unileber Nigeria ya kaddamar da gasar zane-zane don fito da hazakar daliban makarantar sakandare.

Shirin wanda aka yi wa lakabi da ‘Unleash Your Potential’ an kaddamar da shi ne a ranar Juma’a a Legas, kamfanin ya ware miliyan 90 don gudanar da shi, inda daliban da suka samu nasara za su samu kyautar Naira miliyan 1 dukkansu.
Babban Manajan Kamfanin OMO, Sarah Adoki a lokacin da take bude kaddannar da shirin a Legas ta ce sun kaddamar da wannan shiri ne don ganin cewa lokaci ne da ya kamata a tallafa wa daliban sakandare don su cika burinsu.
“Mun kirkiro wannan shirin ne don mun fahimci lokaci ya yi da ya kamata mu tallafa daliban sakandare don su cika burinsu. Babu shakka mun fahimci zuba jari a kan daliban zai taimaki al’umma, don haka OMO ya ce ya kamata iyaye su mayar da hankali a kan ’ya’yansu, saboda suna daya daga cikin wadanda za su taka muhimmiyar rawa don ’ya’yansu su zama mutanen kwarai.” Inji ta.
An bangaren zane-zane ana bukatar daliban makarantu su yi wani zane mai ma’ana da ilimantarwa, ana so su yi zanen a kwalin OMO Fast Action, daga nan ne jakadun kamfanin za su karbi wadannan zane-zanen daga makarantu, a karshe a karrama na daya da na biyu da kuma na uku.
“daliban da suka yi nasara a makarantu za su kara da juna har a samu a samu na daya a jiha. Wadanda suka yi nasara a jihohi kuma za a gayyace su zuwa Legas karkashin kulawar malamai da iyayensu don su fatata a nan. Haka za a fafata har a fitar wanda ya yi na daya a matakin kasa.” Inji ta.
Ta ce a bangaren rubutun makaloli kyaututtukan da na daya da na biyu zuwa na uku za su ci a matakin jihohi sun hada da Laptop da kudi Naira dubu 30 da Naira dubu 20 bi-da-bi. Inda na daya da na biyu da na uku a matakin kasa za su ci Naira miliyan 1 da Naira dubu 500 da Naira dubu 200 bi-da-bi.
Ta ce: “A bangaren rubutun makala ana bukatar daliban su rubuta makala mai taken: ‘Yadda mahaifiyata ta taimake na iya wanke tufafina da Omo’ (How my mum helped me achiebe success by washing my clothes with OMO fast action detergent). dalibai 50 da suka fara mika wannan mukalar ne za su fara samun nasarar lashe kyaututtukan.”