United na da damar kammala Firimiyar Ingila a sahun ’yan hudun farko — Ten Hag

Za mu dage mu ci wasanni uku daga hudun da suka rage mana.

United na da damar kammala Firimiyar Ingila a sahun ’yan hudun farko — Ten Hag

Erik ten Hag ya ce har yanzu Manchester United tana da damar kammala gasar Firimiyar Ingila ta bana a cikin ’yan hudun farko.

Hakan zai bai wa kungiyar Old Trafford buga Champions League a badi kenan, wadda ta kara a Europa League a kakar nan.

Sevilla ce ta fitar da United daga Europa League na bana a zagayen quater finals da cin 5-2 gida da waje.

United tana ta hudu a kan teburin Premier League da kwantan wasa da maki 63, sai dai maki daya ne tsakaninta da Liverpool ta biyar mai maki 62.

Ranar Lahadi West Ham ta doke United 1-0 a wasan mako na 35 a Premier League, hakan ya sa ta kasa komawa ta uku, gurbin da Newcastle take mai maki 65.

Tun kan karawar da West Ham ta ci United, kungiyar Old Trafford ta yi rashin nasara a hannun Brighton 1-0 ranar 4 ga watan Mayu a dai gasar Premier.

“Ya kamata mu ci wasa uku daga hudun da suka rage mana, saboda haka komai yana hannun mu,” in ji Ten Hag.

Ya kara da cewar “Ba wai damar tana wajen Liverpool ba, damar tana tare da mu, kuma komai yana hannun mu.”

Ten Hag ya dauki Caraboa Cup a kakar farko da yake jan ragamar Manchester United, na farko da kungiyar ta dauka tun bayan 2017.

Haka kuma United za ta buga wasan karshe a FA Cup da Manchester City ranar 3 ga watan Yuni a Wembley.