United na kokarin tsawaita kwantaragin Rashford
PSG ta soma zawarcin Rashford da albashi mai tsoka.
Manchester United na shirin fara tattauna batun sabon kwantiragi da dan wasan gabanta Marcus Rashford gabanin karshen wannan kaka.
United ta biijiro da zabin Karin shekara guda a kwantiragin Rashford, wanda zai sa ya ci gaba da zama a kungiyar har zuwa shekarar 2024, amma kuma sun kagara su cimma yarjejeniya ta tsawon lokaci.
- Ku zo mu hada kai don ciyar da Gombe gaba – Gwamna ga ’yan adawa
- Wahalar man fetur ta fara raguwa a Kano
Wasu majiyoyi sun ce United za ta so ta cimma yarjejeniya da Rashford a karshen wannan shekarar, ko kuma a farkon kaka mai zuwa.
Paris Saint Germain ta Faransa ta nuna sha’awar daukar Rashaford a baya, amma ana sa ran dan wasan mai shekaru 25 ya ci gaba da zama a United, inda yake kan ganiyarsa a karkashin mai horarwa Erik Ten Hag.
United na neman dan wasan gaba kafin kaka mai zuwa, sai dai Rashaford yana cikin tsarin mai horarwa, Ten Hag.