United ta casa Bournemouth, Everton ta ji jiki a gida
Arsenal dai ta ci gaba da zama daram a teburin Firimiyar ta Ingila.
A gasar Firimiyar Ingila, kungiyar Manchester United ta ci gaba da jan zarenta tun bayan dawowa daga hutun Gasar Kofin Duniya da aka fafata a Gabas ta Tsakiya.
Manchester United dai a yanzu ta yi zaman dabaro a mataki na hudu, bayan doke Bournemouth a Old Trafford 3-0 ranar Talata.
- DAGA LARABA: Yadda Yaudara Ta Zamo Ruwan Dare A Fagen Soyayya
- Ministan Isra’ila ya kai ziyara masallacin Kudus
Luke Shaw da Casemiro da kuma Rashford ne suka ci kwallayen.
Ita kuwa Arsenal dai ta ci gaba da zama daram a teburin Firimiyar ta Ingila, bayan kurman duro da ta yi da Newcastle.
An buga wasan ne a filin Gunners na Emirates, kuma a karon farko a kakar bana Arsenal ta gaza cin wasa a gida.
A sauran wasannin da aka yi karon battar a ranar Talata, Leicester City dai ta yi rashin nasara har gidanta na King Power a hannun Fulham da ci daya mai ban haushi.
To amma a duk cikin wasannin, Everton ce ta fi jin jiki, bayan da Brighton ta sharara mata hudu a Goodison Park.
An tashi wasan 4-1, kuma ita ce rashin nasara ta uku da Everton ta yi jere a gidanta.
Hakan ya kara saka matsin lamba ga kocin kungiyar Frank Lampard, wanda ya ci wasa daya a cikin tara a bana.