United tana tababa a kan Mourinho

Ga dukkan alamu, kulob din Manchester United na Ingila ya fara tababa a kan ko zai dauki tsohon kocin Chelsea Jose Mourinho a matsayin kocinsa a karshen kakar wasa ta bana ko a’a.Shi dai Mourinho wanda ake danganta shi da komawa Manchester United a karshen kakar wasa ta bana tun bayan da ya raba gari […]

United tana tababa a kan Mourinho
United tana tababa a kan Mourinho

Ga dukkan alamu, kulob din Manchester United na Ingila ya fara tababa a kan ko zai dauki tsohon kocin Chelsea Jose Mourinho a matsayin kocinsa a karshen kakar wasa ta bana ko a’a.
Shi dai Mourinho wanda ake danganta shi da komawa Manchester United a karshen kakar wasa ta bana tun bayan da ya raba gari da kulob din Chelsea, a yanzu kulob din na United ya dawo daga rakiyarsa inda yake tunanin ba mataimakin koci Ryan Giggs dama idan Luois ban Gaal ya ajiye aiki, maimakon Jose Mourinho.
Rahoton ya nuna mahukunta kulob din United ba su gamsu da bayanin da Mourinho ya yi musu ba na cewa da wuya ya kawo sababbin ’yan kwallo idan ya zama kocin kulob din da hakan ke nuna zai cigaba da amfani da tsofaffin ’yan kwallon da ya samu a kulob din ne, maimakon lalubo sababbi.
Sannan mahukunta kulob din suna tababa kan yadda za su kwashe da Mourinho ganin yadda aka shaide shi a matsayin kocin da ba ya tankwaruwa a mafi yawan lokuta.
Don haka akwai alamun murna za ta koma ciki ga magoya bayan kulob din da suke neman a ba Jose Mourinho dama ya zama koci a karshen kakar wasa ta bana.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa