United za ta mayar da Harry Kane mafi tsada a tarihi, PSG za ta gwama Haaland da Mbappe
Manyan kungiyoyi na rububin kulla alaka da dan wasan Napoli, Victor Osimhen.
Manchester United ta dauki haramar mayar da Harry Kane dan wasa dan Birtaniya mafi tsada a tarihi. Kungiyar za ta so raba dan wasan mai shekara 29 da Tottenham a karshen wannan kakar wasan. (Mirror)
Dan wasan gaban Liverpool da Brazil, Roberto Firmino, na iya komawa Amurka domin buga wasannin kwallo da St Louis City ta gasar MLS. Dan wasan mai shekara 31 na da wasu kungiyoyin da suka nuna sha’awar sayensa. (Bleacher Report)
Sai dai Atletico Madrid ta kasance kungiyar da ke kan gaba wajen raba Roberto Firminho da Liverpool da zarar kwantiraginsa ya kare a kungiyar. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Haka kuma, akwai rahoton da ke cewa wata kungiyar kwallon kafa daga Saudiyya ma na son mika wani “tayi mai tsoka” ga Firmino bayan ya bar Liverpool. (Football Insider)
Tottenham na shirin sayen Jordan Pickford na kungiyar Everton a karshen wannan kakar wasan, sai dai golan mai shekara 29 tuni ya sabunta kwantiraginsa da Everton. (Sun)
Paris St-Germain za ta yi yunkurin sayen Erling Haaland, dan wasan gaban Manchester City mai shekara 22 domin hada shi da tauraronta, Kylian Mbappe mai shekara 24. (RMC Sport, via Sport – in Spanish)
Chelsea na shirin dauko Frenkie de Jong, dan wasan tsakiya na Barcelona, a karshen wannan kakar wasan. (Football Insider)
Dan wasan Belgium, Romelu Lukaku na son ci gaba da zama a Inter Milan bayan da wa’adinsa na aro ya kawo karshe, sai dai kungiyar ta Italiya ba za ta iya ci gaba da biyan albashinsa ba ga shi kuma kocin Chelsea Graham Potter bai saka shi cikin ’yan wasan da yake son yin aiki da su ba. (Mail)
PSG ta bi sahun Chelsea da Manchester United wajen farautar Victor Osimhen, dan asalin Najeriya kuma dan wasan gaba na Napoli mai shekara 24. (Nicolo Schira)
AC Milan ta janye daga shirinta na raba Naby Keita da Liverpool, tana cewa karin albashin da dan wasan na tsakiya mai shekara 28 ke bukata ya yi ma ta tsada matuka. (Calciomercato – in Italian)