Usman Kumo, Aliyu Madakin Gini sun zama jagororin Majalisar Wakilai

Shugaban Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas ya bayyana Usman Bello Kumo (APC-Gombe) da Aliyu Sani Madakin Gini (NNPP-Kano) cikin ƙunshin jagororin majalisar. Honorabul Tajuddeen Abbas ya bayyana Usman Bello Kumo a matsayin mai tsawatarwa ɓangaren masu rinjaye. Ya kuma bayyana Aliyu Sani Madakin Gini a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye. Ali Ndume, Rufa’i Hanga sun zama […]

Usman Kumo, Aliyu Madakin Gini sun zama jagororin Majalisar Wakilai

Zauren Majalisar Wakilai

Shugaban Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas ya bayyana Usman Bello Kumo (APC-Gombe) da Aliyu Sani Madakin Gini (NNPP-Kano) cikin ƙunshin jagororin majalisar.

Honorabul Tajuddeen Abbas ya bayyana Usman Bello Kumo a matsayin mai tsawatarwa ɓangaren masu rinjaye.

Ya kuma bayyana Aliyu Sani Madakin Gini a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye.

Ali Ndume, Rufa’i Hanga sun zama jagororin Majalisar Dattawa

Cire Tallafi: Majalisar Wakilai ta bukaci Tinubu ya fito da hanyoyin rage radadi

Sauran jagororin da shugaban majalisar ya bayyana a ɓangaren masu rinjaye sun haɗa da Julius Ihonvbere a matsayin shugaba, Abdullahi Halims mataimakin shugaba, da Adewumi Onanuga mataimakin mai tsawatarwa.

A ɓangaren marasa rinjaye kuma, Honorabul Abbas ya sanar da Kingsley Chinda a matsayin shugaba, Ali Isa mai tsawatarwa da George Ozodinobi mataimakin mai tsawatarwa.