Usman Mu’azu ya yi wa Aminu Saira magaji

A ranar Asabar da ta gabata ne furodusa Usman Mu’azu ya samu karuwar da namiji, inda ya yi wa fitaccen darakta Aminu Saira magaji.Maidakin furodusan ta haihu a asibitin M & M da ke Sabuwar Gandu a Kano da misalin karfe 10:30 na safe.  Mai jego da jaririnta suna cikin koshin lafiya, kamar yadda furodusan […]

Usman Mu’azu ya yi wa Aminu Saira magaji
Usman Mu’azu ya yi wa Aminu Saira magaji

A ranar Asabar da ta gabata ne furodusa Usman Mu’azu ya samu karuwar da namiji, inda ya yi wa fitaccen darakta Aminu Saira magaji.
Maidakin furodusan ta haihu a asibitin M & M da ke Sabuwar Gandu a Kano da misalin karfe 10:30 na safe.  
Mai jego da jaririnta suna cikin koshin lafiya, kamar yadda furodusan ya bayyana wa wakilin Aminiya
Ya ce “Alhamdulillahi, mai jego da jariri suna cikin koshin lafiya. Na rada wa jaririn suna Al-Amin, na yi wa Darakta Aminu Saira magaji ne.”
Ya yi matukar farin ciki dangane da karuwar da ya samu.
“A yau ina cikin farin ciki marar misaltuwa. Ina mika godiyata ga jama’ar da suka taya mu addu’a da kuma wadanda suka turo sakonni ko suka kira ni suna yi mini fatan alheri. Allah Ya saka musu da alheri.”
Za a yi walima a ranar Sallah, inda daga farko aka gayyato Malam Kabir Gombe, amma saboda uzurin da ya bayar, sai aka gayyato Malam Zakariyya Adam, wanda zai gabatar da wa’azi a gidan furodusan da ke Sabuwar Gandu a Kano.
An daura auren furodusa Usman Mu’azu da Zainab Adam ne a ranar Lahadi 28 ga Afrilu, 2013 da misalin karfe 11:00 na safe a unguwar dan Agundi cikin birnin Kano.