Uwa da ’ya

Wata Babarbariya ce mai suna Fannata ta takura wa wani Bafulatni. Da ta gan shi sai ta ce, “kai yarona.” Haka dai har ba ya son zuwa inda take. Ran nan sai ya ce zai yi maganinta, ya je aka yi masa askin tal-kwabo, sol-sol. Cikin dare ya zage sai dan wani fatari a jikinsa, […]

Uwa da ’ya
Uwa da ’ya

Wata Babarbariya ce mai suna Fannata ta takura wa wani Bafulatni. Da ta gan shi sai ta ce, “kai yarona.” Haka dai har ba ya son zuwa inda take. Ran nan sai ya ce zai yi maganinta, ya je aka yi masa askin tal-kwabo, sol-sol. Cikin dare ya zage sai dan wani fatari a jikinsa, ya shafe jikinsa da farar hoda, ya yi fari fat da shi. Ya je har dakinta tana barci ya tashe ta, ta firgita sai ya ce mata: “Tsakanin ke da diyarki Illagana, wace ce babba?” Sai ta ce masa: “Haba, ni ce fa na haife ta, ai ni ce babba.” Sai ya ce mata: “To dama ni mutuwa ce aka aiko ni in dauki babba a tsakaninku.” Da jin haka sai ta ce: “E, to ni ce na haife ta amma fa Illagana ta jima, ta jima, ta jima, ta jima a duniyar nan.”

Daga Abdullahi Musa Hadeja, 07066180429