Uwa da ’yarta sun casa ta, sun yi mata tsirara

Sun yi taron dangi wajen yi wa matar tsirara bayan sun lakada mata duka a kan abin da aka riga aka sasanta su a caji ofis.

Uwa da ’yarta sun casa ta, sun yi mata tsirara

Mata na kece raini

An gurfanar da wata mata da ’yarta a gaban Kotun Majastare da ke Surulere, Jihar Legas, kan zargin yi wata mata tsirara da kuma lakada mata duka.

Ana tuhumar uwar da ’yarta ne da aikata laifin hadin baki da cin mutunci da kuma tada fitina a cikin al’umma.

Lauya mai gabatar da kara ya fada wa kotun cewa, wadanda ake zargin sun aikata laifukan ne a ranar 13 ga Nuwamba a yankin na Surulere.

’Yan sandan yankin sun ce matar da ’yar tata sun yi taron dangi wajen lakada wa daya matar duka tare da mata tsirara nr a kan batun da an riga an sasanta tsakani a ofishinsu.

Laifin da lauyan ya ce ya saba sassa na 168 (1) (d) da 172 da 411 na Kundin Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Legas na 2015 (wanda aka yi wa gyara).

Sai dai wadanda ake tuhumar sun musanta zargin da ake yi musu.

Alakalin Kotun, Misis M. I. Dan-Oni, ta ba da belin wadanda ake zargin a kan N50,000 kowaccensu tare da shaida dai-dai.

Daga nan ta dage ci gaba da shari’ar zuwa ran 9 ga Disamba mai kamawa.

(NAN)