Uwa da ’ya’yanta da suke karyewa ba tare da sun ji zafi ba

Binciken da Mujallar Neurology Brain ta wallafa ya nuna yadda wata mata ’yar kasar Italiya mai suna Letizia Marsili mai shekara 52 da mahaifiyarta da ’ya’yanta biyu da kuma wata kanwarta ba su jin zafin ciwo a jiki ciki har karaya. Bincike ya nuna cewa, daya daga cikinsu ta karye amma saboda rashin jin zafin […]

Uwa da ’ya’yanta da suke karyewa ba tare da sun ji zafi ba
Uwa da ’ya’yanta da suke karyewa ba tare da sun ji zafi ba

Binciken da Mujallar Neurology Brain ta wallafa ya nuna yadda wata mata ’yar kasar Italiya mai suna Letizia Marsili mai shekara 52 da mahaifiyarta da ’ya’yanta biyu da kuma wata kanwarta ba su jin zafin ciwo a jiki ciki har karaya.

Bincike ya nuna cewa, daya daga cikinsu ta karye amma saboda rashin jin zafin ya sa ba ta san ta karye ba.

Iyalan dai suna fama da larurar rashin jin alamar ciwo a jikinsu. Kuma da zarar sun ji ciwo a jikinsu za su ji zafin ne na wasu ’yan dakika sannan su daina ji baki daya, hakan ya sa jikin nasu yake ta lalacewa saboda rashin sanin ko akwai ciwo ko babu a jikin.

Iyalan dai ba su san suna da wata larura ba sai aka gano daga jikin Letizia.

Daya daga cikin iyalan ya tuka kake na tsawon kilomita 15 sai ya fadi ya samu karaya a hannu amma bai san hannunsa ya karye ba. Sauran ’yan uwansa sun dade suna samun karaya amma ba za su iya tuna adadin karayar ba.

Letizia ta bayyana wa majiyar BBC cewa, ita ba ta jin zafin konewa ko ta gane cewa ta samu karaya a kasusuwanta.

“A kullum muna gudanar da rayuwarmu kamar kowane mutum ko ma fiye da sauran jama’a, saboda za a dade kafin mu yi rashin lafiya ko mu ji wani zafi a jikinmu. Mu ba mu jin ciwo ko alamarsa a jikinmu idan kuma muka ji, to zafin na wasu ’yan dakika ne kawai zai tafi,” inji Letizia.

Bincike ya kuma gano cewa, wadannan iyalai ba su yin zufa baki daya sannan suna cin barkono mai yawa ba tare da suna jin zafin komai a bakinsu ba.

Wanda ya wallafa nazarin Dokta James Cod daga Jami’ar Kwalejin Landan ya ce, wadannan iyalan duk suna da duk jijiyoyin da suke aike wa kwakwalwa sakonni sai dai kawai ba sa aiki ne yadda suka kamata.

Akwai yiwuwar wadansu daga cikin iyalan halittarsu za su taimaka wajen jin zafin jikin nan gaba.

Abin da masana kimiyyar suka gano game da irin wannan halittar da take hana kai wa kwakwalwa sako? Masu bincike sun gano cewa, a kowane irin iyali ana iya samun sauyin halittar da kowace da irin yanayin yadda aka halicce ta yadda za ta gudanar da ayyukanta kamar ZFHD2.

An taba yin bincike a kan wasu beraye biyu da ba su da irin halittar da za ta sa su ji zafi a jikinsu, sai dai kawai su ji ta wata hanya daban.

Bayan sun gudanar da wata sabuwar hanyar binciken sai aka gano wata hanyar da take da alaka da irin halittar da ba ta bambance sauyin yanayi a jikin berayen.

Farfesa Aloisi ya ce, a bincike mai yawa da aka gudanar an gano irin halittar da take ba ta iya bayar da damar jin zafi a jikin halitta da dai sauran abubuwan da ke alaka da su, nan gaba za a iya samun ci gaba wajen fito da irin maganin za a iya amfani da shi.

A yanzu dai wadannan iyalan sun yarda cewa su kadai ne masu fama da irin wannan larurar a duk duniya.

Hamas da Isra’ila sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

HOTUNA: Yadda aka yi bikin tunawa da mazan jiya a faɗin Nijeriya

Sanusi zama daram kuma Sarki ɗaya tilo a Kano — Falana

An rantsar da Shugaban Mozambique Daniel Chapo