Uwa ma ba da mama
Mai karatu ya fahimci cewa, wannan labarin da zan bayar, labari ne na gaskiya. Kuma dalilin da ya sa zan bayar da shi, saboda ina son mutane su fahimci yanayin duniya, da kuma halin da mutum kan iya samun kansa a rayuwa, yanayi-bayan-yanayi. Haka kuma ina rokon duk wanda ya karanta shi, ya nemar wa […]
Mai karatu ya fahimci cewa, wannan labarin da zan bayar, labari ne na gaskiya. Kuma dalilin da ya sa zan bayar da shi, saboda ina son mutane su fahimci yanayin duniya, da kuma halin da mutum kan iya samun kansa a rayuwa, yanayi-bayan-yanayi. Haka kuma ina rokon duk wanda ya karanta shi, ya nemar wa wannan matar gafarar Allah.
A shekaru da yawa da suka shude, wani saurayi, ya samu kansa a cikin wani yanayi na jeka na yi ka, ya kasance ba ya iya tabukawa kansa komai na amfani, in ba domin Allah Ya hada shi da wannan matar auren ba. Hakika wannan matar babu abin da zai ce mata face Allah Ya saka mata da alkhairi, Ya yafe mata dukan kura-kuranta, Ya kuma sanya aljanna ta zamo makomarta. Domin ni ma na san yana son ta kuma yana alfahari da ita, zai iya fadar hakan a gaban kowa ma, duk da cewa, shi kansa idan ya tuno da wadancan shekarun biyu da rabi da suka share suna kwanciya a shimfida daya, yakan zargi kansa da abubuwa da yawa, kuma ina fatan Allah Ya yafe masa.
Kun san Hausawa ke cewa ‘’ka so mai son ka‘’ to hakikanin gaskiya, a duk duniya Allah bai hada shi da wadda ta nuna masa soyayya ba tamkar ta. Domin tun a lokacin da ta fara a za idanuwanta a kansa, Allah mai girma Ya jefa mata tsananin soyayyarsa a rayuwa, har ya kasance ta dauki soyayyar duniya ta dora a kansa, ba ta da lokacin mijinta kamar yadda take da lokacinsa. Duk wani muradinta da farin cikinta ya tare kacokan a kansa.
Abin da zai ba ka tsoro ma shi ne, tun a ranar da ta fara ganinsa, zuciyarta ta kasa hakurewa da soyayyarsa, har sai da ta rungume shi a kirjinta, tana mai cike da shauki da dauki a kan wannan sabon masoyi da Allah Ya hada ta da shi a rana tsaka. Abin bai tsaya nan ba, har sai da ta kwana shimfida daya tare da shi a wannan ranar. Kuma daga wancan lokacin, kusan kowace rana hakan ce ta ci gaba da faruwa.
Kusancinsa da ita fa ba zai misaltu ba don har sai da ya kasance ba ta iya rabo da shi ko da na tsawon wuni daya ne, kuma ita ce take yi masa dukkan wata larura ta rayuwa da dan Adam ke bukata, amma a cikin kudin mijinta. Wannan dalilin ne ya sa shi ma ya fara tantancewa da dukanin irin abubuwan alfarmar da take yi masa, har ya fara zamowa, ba ya son kusantar kowa face ita. kamshin jikinta kawai yakan wadatar da shi, kuma ya kwantar da hankalinsa. Har aka wayi gari, idan ta nisance shi, nan take yakan zubar da hawaye, kuma ba zai dawo hayyacinsa ba har sai ya ji ta kusa da shi.
Watakila mai karatu ya yi tambaya, to shi mijinta yana ina? To abin da ya kamata mai karatu ya sani shi ne: Duk da yake cewa mijin nata yakan yi tafiye-tafiye, amma a sane yake da duk abin da ke faruwa a gidansa. Amma ba shi da ikon hana faruwar hakan, saboda haka bai yi yunkurin hakan ba. Kuma hakan ne ya sa aka zauna lafiya har zuwa yau.
To shi me ya sa bai kaurace mata ba? Ba shi da ikon yin hakan ne, saboda tuni ta saye zuciyarsa, kuma ta gama mallake ta. Duk fa larurarsa ita ce mai kula da ita. Idan ya rasa kudi ita ce mai ba shi, ita ce ke kula da dukan abincinsa da abin shansa. Tufafin sakawarsa, daukar nauyin wanke su da goge su! Bayan hakan, idan ba shi da lafiya, ba shi da wanda ke jinyarsa sai ita, duk da cewa, yana da ’yan uwa barkatai. Wannan ne ma ya sa, nake iya cewa, da za a dauki dukan abukansa da ’yan uwansa a dora a sikeli daya, ba za su dauki kashi daya na goman soyayyar da yake mata ba.
Wannan matar ba kowa ba ce face mahaifiyarsa (matar mahaifinsa), Ita ce take matukar so da kaunarsa, tun ranar da ta haife shi, kuma take ta kwanciya da shi a shimfidarta don gudun kada wani abu ya same shi, kuma a hakan take ta dawainiya da shi har tsawon shekara biyu da rabi ba tare da ta kasa ba, har ta yaye shi. Mahaifinsa shi ne mijinta, wanda duk wata larura a cikin dukiyarsa take yi masa, kun ga ai ba zai hana a yi wa dansa larura ba!
Abin da nake nufi da abin da idan ya tuno yakan yi nadama, shi ne: Duk da irin wannan dawainiyar, wasu lokuta yakan saba musu saboda ajizanci na dan Adam. Haka abin yake a wurina, kamar kuma yadda yake a wurin kowa. Mahaifiya ba wasa ba fa! Mu yi la’akari da wannan dawainiyar kawai ta shekara biyu da rabi, har yaushe za mu iya biyan mahaifanmu ladar wannan gwarzon aiki.
Hakika mahaifa (musamman mahaifiya) sun cancanci kowane irin nau’i na biyayya daga wurinmu. Ina fatar Allah Ya albarkaci mahaifiyata da mahaifina da mahaifan masu wannan karatu a kan dawainiyar da suke yi da mu. Allah Ya sa mu gama da su lafiya. Wadanda suka riga mu gidan gaskiya kuwa, Ya Allah Ka jikansu da gafara.
Nasir Abbas Babi ya rubuto daga Sakkwato, za a iya samun sa a wannan lambar :08033186727