Uwa ta dasa itatuwa miliyan biyu don cika wasiyyar danta

Wata tsohuwa ’yar shekara 67 da ta fito daga Shangai ta yi dashen itatuwa miliyan biyu a hamadar da ke Arewa maso Yammacin kasar Sin a tsakiyar Mongolia, cikin shekara 12, don cika wasiyar danta.Dattijuwa Yi Jiefang, mai sadaukar d akai, ta sayar da gidnata, inda ta kafa wata kungiya ta NPO, “Green Life,” don […]

Uwa ta dasa itatuwa miliyan biyu don cika wasiyyar danta
Uwa ta dasa itatuwa miliyan biyu don cika wasiyyar danta

Wata tsohuwa ’yar shekara 67 da ta fito daga Shangai ta yi dashen itatuwa miliyan biyu a hamadar da ke Arewa maso Yammacin kasar Sin a tsakiyar Mongolia, cikin shekara 12, don cika wasiyar danta.
Dattijuwa Yi Jiefang, mai sadaukar d akai, ta sayar da gidnata, inda ta kafa wata kungiya ta NPO, “Green Life,” don dashen itatuwa a hamadar kasar Sin, bayan da ta samu labarin mutuwar danta Yang Ruizhe, a wani hadari d aya yi yayin d ayake karatu a kasar Japan tun a shekara ta dubu biyu (2,000).
dan wannan mata, mai suna Yang ya taba fsda mata burin san a rayuwa, wato idan ya dawo kasar Sin zai himmatu wajen yaki da kwararowar Hamada. Saboda tsananin alhini, wannan uwa sai ta yanke wa kanta cimma burin danta na rayuwa. Ta yi amfani da kudin inshorar danta da diyyar da aka biya ta hadarinsa, tare da kudin da ta samu wajen sayar da gidanta.
Tun daga shekarar 2004, Yi ta yi dashen itatuwa miliyan daya da dubu 100 a kan tundurkin kasa na Keerkin, sannan tad aura aniyar dasa wasu itatuwan a kan kasa mai fadin kilomita dubu takwasa da 660 a kowane bari; ta dasa itatuwan katsako a hamadar ala shan da ke Arewa maso Yammacin kasar Sin.
“Mutane ba za su tafi da kudi ba, bayan sun mutu. Don haka nike kokarin juya kudina su zama korayen tsirrai a doron kasa, al’amarin da zai tsaya tsawon rayuwa,” inji Yi.