Uwa ta fusata ta jefa ’yarta cikin kogi a Bayelsa
A cewar shaidu, Rachael ta je yin wanka a bakin kogi duk da gargaɗin da mahaifiyarta ta yi mata.
![Uwa ta fusata ta jefa ’yarta cikin kogi a Bayelsa Uwa ta fusata ta jefa ’yarta cikin kogi a Bayelsa](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/Bayelsa-State-map.jpg)
A wani rahoto na ibtila’i da ya afku a unguwar Ukubie da ke ƙaramar hukumar Ijaw ta Kudu a Jihar Bayelsa inda wata mata mai suna Madam Stella ta jefa ‘yarta ’yar shekara shida mai suna Rachael a cikin kogi saboda fushi.
A cewar shaidu, Rachael ta je yin wanka a bakin kogi duk da gargaɗin da mahaifiyarta ta yi mata.
- Yadda matar aure ta kashe dan kishiyarta da tafasasshen ruwa
- An sace tsohon Shugaban Hukumar NYSC, Janar Tsiga
“Lokacin da mahaifiyar ta samu ’yarta a bakin kogin, sai ta fusata. Duk da gargaɗin da aka yi mata na ƙauracewa kogin, Rachael ta ƙi, wanda hakan ya sa mahaifiyar tashin hankali ta fusata,” in ji wani ganau.
A cikin fushi, an samu rahoton cewa Madam Stella ta kama hannun Rachael kuma ta jefa ta a cikin wuri mai zurfi a kogin sau biyu, wanda ya kai ga mutuwar ‘yarta.
Bayan faruwar lamarin, jama’ar yankin unguwar da abin ya shafa sun tunkari mahaifiyar, inda ta amsa aikata laifinta, inda ta ce ba ta yi niyyar kashe ɗiyarta ba.
Lamarin da ya jefa jama’ar yankin Ukubie cikin firgici, inda wani ɗan uwansu mai suna Jeph Nation ya bayyana ra’ayinsa.
“Na riga na rasa ‘yan uwa guda biyu a wannan shekara, amma wannan shi ne mafi zafi da ban tausayi,” in ji shi.
Hotunan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna Madam Stella ta furta wannan iƙirari da yaren ƙabilar Ijaw, inda jama’a suka kewaye ta.
A wani bidiyo, an ganta zaune a cikin kwale-kwale da gawar ɗiyarta a gefenta, tana ɗauke da ita.
A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan Jihar Bayelsa, ta bakin kakakinta, DSP Musa Mohammed, ya bayyana cewa har yanzu ba a kai ga sanar da rahoton faruwar lamarin ga ‘yan sanda ba a hukumance.