Uwa ta kai karar mutumin da ya yi lalata da ’ya’yanta 2 a Kano
Wani likita ya duba wadanda lamarin ya shafa, har ya rika fitar da tsutsotsi da yawa a duburarsu.
Mahaifiyar yaran da abokin mahaifinsu ya yi luwadi da su a Kano ta sake maka shi a kotu bayan mahaifinsu ya amince an kashe maganar a kotu.
Mahaifiyar yaran ta bayyana cewa wani likita a daya daga cikin asibitocin jihar ya duba wadanda su, har ya rika fitar da tsutsotsi daga duburarsu, sannan ya dinke wa daya daga cikinsu raunukan da ya samu a sakamakon cin zarafin.
Matar wadda a yanzu take aure a wani waje bayan mutuwar aurenta da mahaifin yaran, ta sake shigar da kara a ofishin ’yan sanda na Jakara da ke Karamar Hukumar Dala, inda ta bukaci a tura su kotu bayan ta gano cewa mahaifin yaran ne ya sa aka janye karar ba tare da wani gamsasshshen bayani ba.
Ta bayyana takaicinta bisa yadda ’yan sanda suka bayar da belin wanda ake zargin kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
“Daya daga cikin yaran wanda har yanzu bai kai shekara takwas ba ya ce mutumin ya sha yin barazanar cutar da su idan har suka fada wa wani abin da yake yi musu.
- Ya Kashe Matarsa Kan Zuwa Ganin Danta A Gidan Tsohon Mijinta
- Mai shanyewar barin jiki ya mutu a gidan mata
“Duk da barazanar da yake yi musu, yaron ya ce, ya sha fada wa mahaifinsu abin da ke faruwa sai mahaifin ya ce su bari kar su yi magana, su yi shiru kar kowa ya sani.
“Yaron ya tabbatar da cewa kafin a yi masa magani, tsutsotsi na fitowa daga duburarsa, dan uwansa kuma baya iya rike bayan gida, idan yana tsaye ko a zune bayan gida na iya fita ba tare da ya yi niyya ba.”
Mahaifiyar yaran ta yi kira ga gwamnan jihar Kano ya sa baki a cikin lamarin domin ganin an yi wa kananan yaran adalci.
Kwamishinar Harkokin Mata, Yara da Nakasassu ta Jihar Kano, Aisha Lawan Saji, wadda ta bayyana baƙin ciki kan halin da yaran ke ciki, ta lashi takobin ganin an hukunta wanda ya yi lalata da su.
Daraktar wayar da kan jama’a a ma’aikatar, Aisha Haruna, ta ce kwamishiniyar ta kadu da jin labarin yaron da aka yi wa dinki a duburarsa sakamakon tsattsagewar da ta yi.
Kwamishinar ta yi alkawarin bin diddigin lamarin har zuwa karshensa.
Ta kuma biya bashin da aka tara na tsawon watanni na kula da yaran wadanda har yanzu ba su gama warkewa daga raunukan da suka samu a duburarsu ba.