Uwa ta kashe danta ta dafa kansa

Matar ta shaida musu cewa ta dafa kan dan nata ta ci ne saboda “tana so ya kasance tare da ita har abada.”

Uwa ta kashe danta ta dafa kansa

Jariri

Wata mata ta kashe danta mai shekara biyar, ta daddatsa sassan jikinsa sannan ta dafa naman kansa ta ci.

’Yan sanda sun cafke matar mai shekara 29 ne bayan sun gano sassan jikin dan nata a cikin bokiti a gidanta da ke birnin Faqus a lardin Ash Sharqiyah na kasar Masar.

Kafar yada labarai ta Masrawy da ke kasar ta ruwaito cewa makure yaron matar ta yi, ta kashe shi sannan ta daddatsa sasan jikinsa.

An ruwaito cewa kawon mamacin ne ya faro gano abin da ya faru a lokacin da ya ziyarci gidanta, sannan ya sanar da jami’an tsaro.

A ranar Juma’a ’yan sanda sun bayyana cewa matar, mai suna Hanaa ta shaida musu cewa ta dafa kan dan nata ta ci ne saboda “tana so ya kasance tare da ita har abada ,” ko ya sake  komawa mahaifarta.

Hanaa wadda ta aurenta ya dade da rabuwa ta shaida wa ’yan sanda cewa ba da gangan ta kashe dan nata mai suna Youssef ba, tabin hankalin da take fama shi ne ya sa ta aikata hakan.

Kafar Masrawy ta ce an gurfanar da Hanaa a gaban kotu, kuma za a yi mata gwajin kwakwalwa domin tantance lafiyar hankalinta.