Uwa ta rasu a wurin raba fada tsakanin ‘ya’yanta a Abuja

Matar mai suna Zainab Ibrahim ta rasa ranta ne bayan daya daga cikin ‘ya’yan nata da ke fada da juna ya soka mata wuka….

Uwa ta rasu a wurin raba fada tsakanin ‘ya’yanta a Abuja

Zanen kisa

Wata mata ta gamu da ajalinta a yayin da take kokarin raba fada tsakanin ‘ya’yanta a Yankin Birnin Tarayya.

Matar mai suna Zainab Ibrahim ta rasa ranta ne bayan daya daga cikin ‘ya’yan nata da ke fada da juna ya soka mata wuka a bisa kuskure.

Wani mazaunin yankin Kpaduma da ke unguwar unguwar Asokoro a Abuja, inda lamarin ya faru, Saliu Shehu ya ce an garzaya da ita zuwa asibiti amma daga baya ta ce ga garinku nan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Birnin Taraya, Josephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin, wanda ta ce ana bincike a kai.

Sai dai ta bayyana cewa dan da ake zargi da soka wa mahaifiyar tasa wuka ya cika wandonsa da isa.