Uwa tagari

Daga cikin muhimman abubuwa a Musulunci da suke taka muhimmiyar rawa ga tarbiyyar yara ita ce uwa, domin dukkannin wani tasiri da yaro yake samu to yakan samu a karkashin iyayensa, tasirin kan fara ne tun daga lokacin da aka dauki ciki har zuwa balaga. Ruwaya ta zo daga jikan Manzo Sayyadina Ja’afar Assadik daga […]

Uwa tagari

Daga cikin muhimman abubuwa a Musulunci da suke taka muhimmiyar rawa ga tarbiyyar yara ita ce uwa, domin dukkannin wani tasiri da yaro yake samu to yakan samu a karkashin iyayensa, tasirin kan fara ne tun daga lokacin da aka dauki ciki har zuwa balaga.

Ruwaya ta zo daga jikan Manzo Sayyadina Ja’afar Assadik daga Manzo S.A.W ya ce “Farin ciki ya tabbata ga wanda mahaifiyarsa ta kasance kamammiya”.

Ka ga kenan samun Uwa tagari kamammiya me kyan hali da dabi’a  yana da tasiri ga tarbiyyar yara. Idan aka samu uwa mai tausayi da hankali da Ilimi da sanin yakamata, wacce mijinta ke ganin girmanta da darajarta to wannan yana da tasiri a cikin tarbiyyar yara da halayensu.

Lallai idan uwa ta kasance mai daraja da kima a wajen mijinta to hakan zai samar mata da kwanciyar hankali da nutsuwa da zai taimaka kwarai da gaskiya wajen tarbiyyar yara, lallai uwa da ba ta samu wannan ba, to hakika za ta kasance kodayaushe cikin fada da ganin laifin kowa da huce haushi akan ‘yayanta, kuma yana iya sanyata la’ana ko zagin wadannan yara da zaluntarsu, wanda hakan zai iya haifar masu da mummunar al’ada da za su tashi da ita a rayuwarsu, kuma suna iya zama alakakai ga al’umma su zama tamkar wata guba a cikinta, ka ga rashin nutsuwa da kwanciyar hankalin ne ya yi tasiri  a cikin rayuwar ’ya’yanta.

Babu shakka samun nagartacciyar uwa a cikin al’umma abu ne mai matukar muhimmancin da yakamata maza su  yi la’akari da shi wajen neman aure, domin da mace tagari ne al’umma ke zama lafiya kuma abin alfahari da koyi ga kowa.

Ibrahim Hamisu 08060651676  ya rubuto daga Kano