Uwar da ta jefo danta ta dirko daga dogon bene ta bar wasikun neman afuwa

Wata uwa ta jefo danta daga farfajiyar dogon bene da ke rukunin dogwayen gine-ginen tafkin Jumeirah kafin ta dirko ta biyo shi, inda ta bar wasikun neman afuwa ga mijinta da ’yan sanda a Dubai. Wannan uwa wadda asalinta daga Turai ta fito tana fama amatsanancin ciwon tabin kwakwalwa, don haka da ta fahimci danta […]

Uwar da ta jefo danta ta dirko daga dogon bene ta bar wasikun neman afuwa

Wata uwa ta jefo danta daga farfajiyar dogon bene da ke rukunin dogwayen gine-ginen tafkin Jumeirah kafin ta dirko ta biyo shi, inda ta bar wasikun neman afuwa ga mijinta da ’yan sanda a Dubai.

Wannan uwa wadda asalinta daga Turai ta fito tana fama amatsanancin ciwon tabin kwakwalwa, don haka da ta fahimci danta na fama da cutar daji, sai ta yanke hukunci salwantar da rayuwarta da tashi. Wannan al’amari dai ya auku ne a rukunin gidajen Jumeirah Lake Towers farkon Oktobar bana.

Daraktan kula da wuraren da aka aikata miyagun laifuka na Hukumar ’yan sandan Dubai, Laftanar-Kanar Ahmad Hameed Al Merri.

“Mun yi nmazarin hotunan kyamarar tsaro ta CCTb da ke jikin ginin daura da wani otal, sai muka ga uwa ta yi jifa da danka, inda daga bisani ta yi tsalle ta dirko. Babu wani kullin makirci a wannan lamari,” inji Laftanar -Kanar Al Merri.

’Yan sandan Dubai sun ce gawarwakin uwar da danta tuni aka kai su dakin bincike. Kuma jami’an bin kadin miyagun laifuka da aka aikata sun yi nazarin hujjojin da suka tabbatar da aukuwar lamarin.

“Mun dauka akwai wani kullin makirci a wannan lamari, amma hoton bidiyon ya nuna hakikanin abin da ya faru. Ta baro wata masarautar (cikin masarautun Hadaddiyar Daular Larabawa – UAE) tare da danta, sai ta kama hayar daki kafin  ta halaka kanta,” a cewar Laftanar-Kanar Al Merri.

Wannan uwa ta bar wasiku biyu, daya ga mijinta, inda ta nemi afuwarsa kana bin da ya faru, dayar kuwa ta rubuta ne ga ’yan sandan Dubai, inda ta yi musu bayanin cewa ba za ta iya ci gaba da rayuwa ba, ganin danta na fama da ciwon daji.

“Alamun yatsun hannun da aka samu a farfajiyar benen  na uwar ne. Sai muka kira mijinta, wanda ya yi matukar kaduwa, tare da rashin yardarm cewa matarsa ta jefo dansu daga sama ta dirko sun mutu tare,” kamar yadda Laftanar-Kanar Al Merri ya yi karin haske kan lamarin.

DAGA LARABA: Me Ya Sa ’Yan Najeriya Suke Buga-Buga Ko Da Suna Aikin Albashi?

UNICEF ta tallafa wa Kano da kayan adana alluran rigakafi

Ambaliya: BUA ya bai wa Maiduguri tallafin biliyan 2

’Yan sanda 5 sun rasu a hatsarin mota a Kano