Uwar tagwaye ta yi wa daya zanen tattoo don bambance su

Wata mahaifiyar tagwaye ta fusata surukarta, saboda gaza tantance sunayen tagwayen da ta haifa, har sai da ta yi wa daya daga cikinsu zanen tattoo. Matar mai shekara 31 ta haifi tagwaye masu suna Adam da Jack, amma har bayan shekara biyar ta gaza bambance su saboda kamanninsu ya yi wa. ‘APC na bukatar mulki […]

Uwar tagwaye ta yi wa daya zanen tattoo don bambance su

Wasu tagwaye masu kama da juna

Wata mahaifiyar tagwaye ta fusata surukarta, saboda gaza tantance sunayen tagwayen da ta haifa, har sai da ta yi wa daya daga cikinsu zanen tattoo.

Matar mai shekara 31 ta haifi tagwaye masu suna Adam da Jack, amma har bayan shekara biyar ta gaza bambance su saboda kamanninsu ya yi wa.

Jack an haife shi da wani ciwo da hakan ya sa za a rika yi masa allura sau daya duk mako, sanadiyyar rashin iya bambance su, sai ta yanke shawarar yi wa mai larurar zanen tattoo don saukin gane shi idan za a yi masa magani, saboda kada a yi kuskuren yi wa Adam allurar, kamar yadda jaridar Daily Star ta ruwaito.

A yayin da take bayanin abin da ya tilasta ta yin alamar ta ce, idan ta tafi wajen aiki surukarta ce ke kula da tagwayen, wani lokaci an zo yi wa Jack allura sai aka yi kuskuren yi wa Adam.

“Surukar ta yi kuskuren mika mai lafiya a matsayin mara lafiya,” inji ta.

“Kamanninsu ya yi yawa, ko mahaifin tagwayen bai iya saurin bambance su, kamar yadda kowa yake yi idan ya gan su tare.

“Ta yi saurin gano kuskuren da ta aikata don haka ta yi saurin kiran masu ba da agajin gaggawa ta lambar 911 daga nan aka mika su asibiti.

“A lokacin da na je asibitin an bai wa Adam maganin da zai amayar da wanda aka ba shi, na samu duka tagwayen cikin annashuwa suna shan lemun kwalba.”

“Surikar tawa tana gefe, na yi kokarin kwantar mata da hankali, amma ta ki amincewa da hakan,” inji mahaifiyar tagwayen.

Don dakatar da aukuwar irin haka nan gaba, sai ta ce likita ya shawarce ta kan ta yi wa mai ciwon zanen tattoo a jikinsa karami kamar girman abin goge rubutun fensir a jikin fatarsa da za a yi saukin ganewa.

A cikin shekara biyu zuwa uku, lokacin da jariran suka fara girma sai zanen ya fara kodewa.

Bayan surukar ta gano abin da aka yi wa tagwayen, sai wata rana Iyayen tagwayen suka nemi tabbatar surukar ta fahimta, inda a kwantar da tagwayen a kasa sannan aka ce ta zabo Jack ta nuna alamar zanen da aka yi masa.

“Ta dauko Adam, sannan ta mika mata Jack bayan minti 20, amma ta gaza tantance su,” inji mahaifiyar.

Mahaifiyar tagwayen ta wallafa rahoton tagwayenta a shafin Intanet na Reddit don masu karatu su tabbatar da cewa, ta yi abu mai kyau-kuma sun fahimta.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya