Uwar yarinyar da aka sare wa kai za ta fuskanci tuhumar laifin sakaci – ’Yan sanda
Jami’an ’yan sanda a kasar Malesiya na duba yiwuwar gurfanar da wata uwa a gaban kotu, a daidai lokacin da take fama da jimamin sare kan diyarta, ’yar shekara biyu. ’Yan sandan sun ce za su tuhumi wannan uwa da laifin sakaci, inda ta bari aka sace ’yarta a kusa da Kogin Klang.Wata majiya kusa […]
Jami’an ’yan sanda a kasar Malesiya na duba yiwuwar gurfanar da wata uwa a gaban kotu, a daidai lokacin da take fama da jimamin sare kan diyarta, ’yar shekara biyu. ’Yan sandan sun ce za su tuhumi wannan uwa da laifin sakaci, inda ta bari aka sace ’yarta a kusa da Kogin Klang.
Wata majiya kusa da jami’an binciken, ta ce, an samu bayanai mabambanta da suka saba wa juna, a daidai lokacin da aka bukaci mahaifiyar wannan yarina, mai suna Siti Salamy Suib, ’yar shekara 32, ta bayar da bayananta. Ta yi zargin cewa ta bar ’yarta tare da kawayenta, saboda za ta shiga bandaki a katafaren kantin sayar da kaya na Kota Raya.
Da ta fito daga bandaki bayan minti biyar, Madam Siti Salmy ta yi ikirarin cewa, ’yarta Siti Soffea Emelda Abdullah, ba ta tare da kawayenta, sai kawai ta shiga nemanta. Ta ce, ta kuma samu labarin abin da ya auku ne, lokacin da jami’an ’yan sanda suka ganota. Suka sanar da ita cikin dare.
“Da muka duba kyamarar sa’ido ta CCTb, mun gano cewa yarinyar tana wasa ne ita kadai, har lokacin da aka saceta. Babu wasu kawaye a tare da ia. Ta yiwu akwai kawayen, kuma uwar na kokarin boye laifinta,” a cewar majiyar ’yan sanda. Kuma majiyar ta bayyana cewa, mai gadi yana kallo aka sace yarinyar, kuma da aka tuntube shi, sai ya ce, ya saba ganin yarinyar tamna wasa da yara, sannan ita da mahaifiyarta ba baki ba ne a wannan wuri.
Shugaban sashen binciken asiri na ’yan sanda, Mataimakin Kwamanda Gan Kong Meng, ya ce har yanzu ’yan sanda na cike da mamakin kan dalilin sare kan Siti Soffea, inda daga bisani aka tsinci gawar makashinta a titin Bandar, bayan da ya nutse a ruwa aka tsamo gawar shi.
“Har yanzu ba mu gano manufarsa ta yin wannan kisan ba. Muna bukatar lokaci don gudanar da bincike. Muna binciken wannan laifi ta kowace fuska, bayan da muka tattara bayanai daga wajen iyayen Siti Soffea, da kuma wadanda suka santa,” inji shi.