Uwargida: Ki san makiyanki na ainihi!
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. A wannan makon in sha Allahu za mu yi wa uwargida bayani kan yadda za ta morewa zama da maigidanta, musamman a Ramadan. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin. Makiyan Ainihi: Duk macen auren da za a tambaya ta […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. A wannan makon in sha Allahu za mu yi wa uwargida bayani kan yadda za ta morewa zama da maigidanta, musamman a Ramadan. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
Makiyan Ainihi: Duk macen auren da za a tambaya ta lissafo manyan makiyanta na gidan duniya, zai yi wuya a ji ta kirgo su a ciki, alhali kuwa su ne mafiya munin makiya! Domin in har ta yi sakaci su ne za su zama sanadiyyar rashin dacewarta da babban rabo a ranar lahira. Allah SWT Ya bayyanar mana makiyanmu na ainihi a cikin littafinsa Mai Tsarki:
“Ya ku wadanda suka yi imani, Lallai daga cikin ma’auratanku (matan aurenku ko mazan aurenku) da ’ya’yanku akwai makiya a gare ku; sai ku kiyaye su…”- Suratul Taghabun, Aya ta 14.
Don haka ki sani ya ke uwargida, maigidanki da kike so, kika bai wa muhimmanci sama da kowa da ’ya’yanki da kike ji da su, wadanda kika daukaka jin dadinsu sama da naki, su ne makiyanki na ainihi! Duk kuwa da cewa ba su kin ki a zuciyarsu, kuma ba su yi miki mummunan fata, amma a fakaice manyan makiyanki ne, domin in kika yi sake sai su jaza miki asarar da wani bayyanannen makiyinki ma bai jaza miki ita ba, wannan shi ne rashin dacewa da babban rabo ranar Lahira. Don haka, kamar yadda Allah SWT Ya umarci ki kiyaye su, sai ki kiyaye ya ’yar uwa, domin wannan shi ne babban gatan da za ki yi wa kanki da iyalinki.
Lakanin da zai ba ki galaba a kan makiyanki:
Lakani daya ne zai ba ki cikakkiyar galaba a kan makiyanki a duniya da lahira, wannan lakani mai tsananin girma ne, mai saukin aikatawa kuma mai tsananin tasiri ga samun nasarar rayuwa a duniya da lahira. Wannan lakani shi ne, riko da Allah shi kadai ba tare da hada Shi da kowa ko komai ba; riko da Allah ya kunshi sa Allah a gaba da ba Shi muhimmanci a zuciya a aikace sama da komai a cikin rayuwa, ta yadda Shi kadai za ki bi a cikin dukkan al’amuran rayuwarki; watau ba za ki bi son ranki ba, ko son ran maigidanki ko na ’ya’yanki ba. Idan kika dawwama cikin aikata haka ’yar uwa, tabbas Allah SWT Zai ba ki kariya daga sharrin wadannan makiyanki, Zai daukaka rayuwarki. Wannan shi ne babban lakanin samun galaba ga makiyanki; sauran bayani da zai zo duk yana kara jaddadar da wannan babban lakanin ne.
Yadda Za ki zauna da makiyanki: Bayan Allah SWT Ya bayyana miki makiyanki na ainihi, Bai bar ki haka ba, Sai da Ya sanar da mafi kyawun hanyoyin da za a mu’amalance su, don ya kasance ba su zama sanadiyyar halakarki a rayuwar duniya da lahira ba; inda Yace:
“…Idan kun yi afuwa, kuma kuka kau da kai kuma kuka gafarta, to lallai Allah Mai gafara ne mai jin kai.”
Wadannan sinadarai uku: afuwa, kau da kai da kuma gafara su ne sinadaran kyakkyawar dangantaka. Idan kika yi la’akari za ki fahimci wadannan sinadarai suna umartar ki da abu daya ne kawai: watau yadda za ki saukaka mu’amalarki da su. Don haka ga bayani kan yadda za ki yi amfani da wadannan sinadarai wajen saukaka mu’amalarki da wadannan mutane mafi muhimmanci gare ki:
Afuwa: Na nufin goge laifi gaba daya ya zama kamar ba a taba aikata shi ba. Don haka in kina so ki zama mowa a wajen maigidanki, ki zama tauraruwar uwa wajen ’ya’yanki, dole sai kin zama mai yi musu afuwa a ko da yaushe. Yin afuwa ba yana nufin rashin nuna wa maigida kuskurensa ba yayin da ya kuskure, ko rashin yi wa ’ya’ya yayin da suka yi laifi, yin afuwa gare su yana nufin hana wannan laifin ya yi tasiri a cikin mu’amularki da su nan gaba. Kada ki ce don maigida ya yi miki wani laifi ke kuma za ki rage kyautatawarki gare shi, sai ki yi masa afuwa, ki ci gaba da kyautata masa kamar yadda kike yi kafin ya yi miki wannan laifin, ko kuma sama da haka, wannan shi ne cikakkiyar afuwa.
Wannan wata da muke ciki mai alfarma watan afuwa ne, na san ba za ki rasa sanin Hadisin nan na Uwar Muminai A’isha RA, inda ta tambayi Annabi SAW cewa “Ya Manzon Allah, in na samu daren lailatul kadari me zan fada a cikinsa? Sai SAW Ya ce da ita, ta rika fadar wannan addu’ar: “Allahumma innaka afuwwun, tuhibbul-‘afwa fa’fu ‘anni.” Ma’ana: “Ya Allah! Kai mai yawan afuwa ne, kuma kana son afuwa, don haka Ka yi mini afuwa.”
Kin ji ’yar’uwa cewa Allah Yana son afuwa, ga shi mun shiga cikin wadannan kwanaki masu tsada na karshen Ramadan, wadanda Annabi SAW Ya ce mu rika yawan rokon afuwa ga Allah SWT, don haka ki rika rokon afuwar laifukanki kamar yadda Manzon Allah SAW Ya umarta, sannan kuma ke ma ki yi rika yin afuwa, musamman ga wadannan mutane da suke mafi kusanci gare ki, watau mijinki da ’ya’yanki.
Ga yadda za ki yi afuwa cikin sauki:
Ki samu littafi da alkalamin rubutu, ki zauna ki rubuta dukkan laifuffukan da kika san maigidanki ya taba yi miki tun farkon da kika san shi har zuwa yau da kike wannan rubutun, bayan kin gama sai ki bi ki bi su daya bayan daya kina gogewa, tare da fadar: “Na yafe masa, na yi masa gafara, na yi masa afuwa, na goge wannan laifi a zuciyata kamar yadda iska ke goge sawun tafiya a sahara…” Haka za ki rika yi har sai kin goge laifuffukan nan, bayan kin yi haka za ki ji dadi da aminci sun sauka cikin zuciyarki, kuma za ki ji so da kaunar mijinki sun dawo sabo fil cikin zuciyarki. Ki daure ki gwada yin haka ki gani, ko da kina ganin ke ba mai rikon laifi ba ce. Haka za ki yi ga ’ya’yanki da na kishiyoyinki idan akwai.
Kau Da Kai:
Na nufin yawan kau da kai ga kananan laifuffuka na yau da kullum, kada ki zama mai yawan sa ido don gano kuskuren mijinki ko ’ya’yanki. Kamar yadda ake cewa: ‘sa ido sana’ar banza.” Don haka idan kika zama mai sa ido, ba ribar da wannan sa ido zai haifar miki sai kunci da yawan bacin rai da korar aminci daga cikin gidanki.
Gafara:
Ita ce yafe laifin da aka yi ko da kuwa ba a share laifin aka mai da shi kamar ba a taba aikata shi ba. Gafara na nufin ba ka rikon mutum da laifin da ya yi kuma ba ka bari wannan laifi ya yi tasiri ga yadda kake mu’amulantarsa ba tun farko.
Wadannan sinadarai dukkansu ’yan ko da yaushe ne, ba wai a yi su sau daya, biyu ko uku kawai ba, ko kuma a ce ‘ni na yi iya yi na haka nan,’ ana yin su ne har abada. Tabbas, wannan sinadarai in kika kika rike su, ba za ki taba samun matsala da maigidanki ko ’ya’yanki ba. Ballantana idan kika gauraya su da makamashin ruhin mai tsada, watau niyya, ki kudure a ranki cewa kina yin haka ne don Allah da neman yardarSa, za ki samu aminci da zaman lafiya a cikin iyalinki.
Don haka ki daure wajen yaki da zuciyarki, kada ki bari wadannan mutane da suka fi kowa muhimmanci a rayuwar duniyarki su zame miki fitina. Da fatan Allah Ya sa mu fi karfin soyen-soyen zukatanmu a kodayaushe, amin.