Uwargida ta kashe damisa a fafatawar da suka yi
Wata mata, mai suna Kamla Debi, a kasar Indiya ta bayyana wa tashar talabijin ta CNN-IBN yadda ta fafata fada da damisa har ta samu nasarar halaka wannan dabba, bayan da ta yi mata kyakkyawan bugu da lauje.Wannan uwargida ’yar shekara 56, tana kwance a asibiti, inda take murmurewa a sakamakon raunukan da ta samu […]
Wata mata, mai suna Kamla Debi, a kasar Indiya ta bayyana wa tashar talabijin ta CNN-IBN yadda ta fafata fada da damisa har ta samu nasarar halaka wannan dabba, bayan da ta yi mata kyakkyawan bugu da lauje.
Wannan uwargida ’yar shekara 56, tana kwance a asibiti, inda take murmurewa a sakamakon raunukan da ta samu a fadan da suka yi da damisar. Ta bayyana wa tasdhar talabijin din cewa. Ta shafe rabin sa’a tana fada da damisar, har dai ta samu ta kasheta, bayan kyakkyawan dukan da ta yi mata, inda ta caka wa damisar lauje.
“Damisar ta so ta cinye ni a lojkuta da dam, saboda haka muka yi ta fafata fada na tsawon lokaci,” kamar yadda ta bayyana wa tashar talabijin din a hirar da suka yi, a gadonta na asibiti da ke Arewacin Jihar Uttarakhand, inda aka daure gwiwar hannayenta da bandeji, a sakmakon raunukan da ta samu a karon battar da suka yi.
“Na rike laujena kankam, ina ta fada da shi, ta haka na samu na kashe damisar,” inji matar, mai suna Kamla Debi.