Uwargida ta kashe mijinta saboda amarya
’Yan sanda a Jihar Osun sun kama wata matar aure mai suna Omotayo Salawudeen da ake tuhuma da laifin kashe mijinta mai suna Alhaji Salawudeen Hakeem saboda ya auro mata kishiya. An kama ta ne tare da wani dan daba mai suna Oladapo Dolapo da tayi hayarsa domin ya taimaka wajen kashe mijin na ta. […]
’Yan sanda a Jihar Osun sun kama wata matar aure mai suna Omotayo Salawudeen da ake tuhuma da laifin kashe mijinta mai suna Alhaji Salawudeen Hakeem saboda ya auro mata kishiya. An kama ta ne tare da wani dan daba mai suna Oladapo Dolapo da tayi hayarsa domin ya taimaka wajen kashe mijin na ta.
Da yake nuna Omotayo da Dolapo a gaban taro da ‘yan jarida a ofishinsa a garin Osogbo, Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Osun, Mista Olafimihan Adeoye, ya ce, dan uwan marigayin mai suna Adesina shi ne ya kai rahoton kisan gillar da aka yi wa yayansa ga ofishin ‘yan sanda. Adesina ya shaida wa ‘yan sanda cewa a ranar 12 ga watan Mayu da ya wuce ne da misalign karfe 3 na dare wasu mutane 2 da ba a san ko su wane ne ba suka shiga cikin gidan marigayi Alhaji Salawudeen Hakeem suka kashe shi ba tare da sun dauki komai daga cikin gidan ba.
Cikin tattaunawa da ’yan jarida a inda ake tsare da ita a hedkwatar ’yan sanda a Osogbo, Uwargida Omotayo mai shekaru 39 da haihuwa da ’ya’ya 3 da ta Haifa da mijin na ta ta furta da bakinta cewa, “bayan saduwa da miji na cikin wannan dare ne sai na gayyato wannan mutumi Dolapo daga wurin da yake boye a cikin gidan muka shiga cikin dakin da miji na yake kwance yana barci na dauki matashin kai (pillow) na toshe bakinsa shi kuma Dolapo ya rinka daba masa sharbebiyar wuka a sassan jikinsa har ya mutu.”
Ta ce ta aikata haka ne saboda mijin na ta ya yi watsi da ita tun daga lokacin da ya auri mata ta 2 a farkon shekarar da wuce. “Ya daina shigowa gida na kuma ya daina saduwa da ni kamar yadda ya saba. A takaice kyakkyawar dangantaka da muka yi shekaru 18 da shi ta sukurkuce babu sauran soyayya tsakaninmu. Na taba daukar jarka cike da man fetur na dumfari gidan da amarya ta ke zaune da nufin kashe ta amma ban yi nasara ba. Yanzu na gane kuskure na kuma na yi nadama tare da neman ’yan Najeriya su yafe mani.”
Shi kuwa dan daba Dolapo cewa yayi, “wannan mata ta zo waje na tayi min bayanin cewa tana so a kasha mijinta saboda ya yi mata laifi day a auro mata amarya bayan shekaru 19 suna tare. Ta ce tun daga lokacin da amaryar ta tare sai mijin na su ya dakatar da daukar dawainiyar abubuwan rayuwa na ita kanta da ’ya’yansu guda 3 shi yasa take so ta raba shi da ransa. Na tambaye ta cewa wace riba za ta samu daga aikata hakan? Sai tace kada in damu akwai babbar riba da za samu.”
Dolapo ya ci gaba da cewa, “a nan take na amince tare da shaida mata cewa zan gudanar da aikin ne tare da taimakonta kuma za ta biya ni ladan aiki naira dubu dari 3 wanda ta fara biya na naira dubu 10 da alkawarin biya mani dukkan bukatu na a nan gaba bayan mun yi nasara. Sai ta gayyace ni zuwa gidan da na shiga ta bayan gida ba tare da kowa ya ganni ba ta kai ni wani sashe ta boye ni har zuwa lokacin da mijin ta ya dawo. Da karfe 1 na dare a lokacin yana barci a cikin dakinsa sai tazo ta kira ni a inda ta dauki matashin kai ta rufe bakinsa ni kuma na daba masa wuka a jikinsa har ya mutu.”
Wannan dan daba ya ci gaba da shaidawa ’yan jarida cewa, a yayin da ya cika aikinsa zai fita daga gidan sai ya ajiye wata takarda mai kunshe da rubutu kamar haka “Aye Ademen” na dora a bisa kirjin mamacin ta yadda za a yi zaton ’yan kungiyar asiri ne suka yi kisan ba daga cikin gida ba.”
Ya ce “a lokacin da zan fita sai na jefar da rigar singileti da nake sanye da ita a kan katangar gidan kuma na gaya mata cewa dole ne ayi alamar balla kofar shiga cikin gidan domin idan ’yan sanda sun zo bincike su gane cewa daga waje aka zo aka yi kisan ba daga cikin gida ba. A wannan lokaci ne wannan mata ta dauko wata rigar singileti da jallabiya ta ba ni na sanya nayi tafiya ta.”