Uwargida ta kona mijinta da amaryarsa

Ta cimma musu wuta a yayin da suke tsaka da cin amarci.

Uwargida ta kona mijinta da amaryarsa

Wuta
Hoto Daga Premium Times

Wata matar aure ta shiga hannu bisa zargin ta da kona kishiyarta da mijinta ta hanyar cinna musu wuta a dakin da suke kwance.

Ita dai amaryar wadda jikinta ya sale baki daya a sanadiyar wutar, kwana 9 ke nan da daura masu aure da mijin nata wanda shi ma gefen jikinsa ya sale, a wannan wutar da aka cinna musu.

Wannan abu ya faru ne a kauyen Sheni da ke Karamar Hukumar Lere a Jihar Kaduna.

Wasu mutanen da suke zaune a gidan da wannan al’amari ya faru ne sun zargi uwargidar da yin wannan aika-aika bisa kalaman da ta rika yi, kafin faruwar wannan al’amari kamar yadda suka bayyana.

Da yake bayyana wa Aminiya yadda al’amari ya faru a kan gadon da yake kwance a asibiti, mijin matar ya ce an cinna wutar ce ta kofar dakinsu da misalin karfe 12 na daren ranar Lahadin makon jiya.

Ya ce suna zaune a bakin gado sai ya ga wuta a kofar dakinsu.

Nan take ya tashi zai bude kofar dakin, sai ya ya gagara, sakamakon haka ne ya kone a gefan hannunsa.

Ya ce ya sake komawa zai bude dakin amma ya sake gagara.

“Sai matar tawa ta bude tagar dakin, sai na ce bari na fara tura ki ki fita, sai ta ce a’a kai ka fara fita.

“Na yi kokarin in fara tura ta, sai ta ce a’a, ni ne zan fara fita, sai na cusa kaina tana turo ni, wani kanina yana ja na daga waje.

“Bayan da na fita aka yi kokarin a fito da ita, abu ya gagara, sai da wutar ta gama ci sannan aka fito da ita.

“Daga nan aka dauko mu zuwa asibiti.”

Ya bayyana cewa kwana 9 ke nan da daura musu aure da amaryar tasa aka sanya musu wuta.

Magidancin ya ce da alama an sanya wutar ce daga kofar dakin nasu amma ba zai iya cewa ga wanda ya sanya wutar ba.

Ya ce yana da mata biyu, baya ga amaryar tasa da aka sanya musu wuta tare.

Amma daya daga cikin matan nasa, ta yi tafiya a lokacin da wannan al’amari ya faru.

A lokacin wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ASP Mohammed Jalige, domin jin ta bakinsa kan wannan al’amari amma ya ce a sake kiran sa.

Sai dai kuma daga baya da akasake kiran sa a waya ba a same shi ba.

Amma wata majiya a ofishin ’yan sanda na garin Saminaka ta tabbatar wa wakilinmu cewa tuni jami’an ’yan sandan sun kama matar da ake zargin, suna shirye-shiryen tura ta zuwa Kaduna, don a ci gaba da bincike.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya