Uwargidan Gwamnan Kebbi ta shawarci mata su nemi ilimi
Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Asma’u Sa’idu dakingari ta shawarci mata su tashi tsaye wajen neman ilimi domin su taimaka wa mazajensu, kuma su samar da kyakkyawar tarbiyya ga ’ya’yansu.Wata takarda da aka raba wa manema labarai dauke da sa hannun Babban Sakataren Watsa Labarai na Gwamnan Jihar ce ta bayyana haka, inda ta ce […]
Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Asma’u Sa’idu dakingari ta shawarci mata su tashi tsaye wajen neman ilimi domin su taimaka wa mazajensu, kuma su samar da kyakkyawar tarbiyya ga ’ya’yansu.
Wata takarda da aka raba wa manema labarai dauke da sa hannun Babban Sakataren Watsa Labarai na Gwamnan Jihar ce ta bayyana haka, inda ta ce Uwargidan Gwamnan ta nuna cewa lokaci ya wuce da mata za su zura wa mazajensu ido su biya masu dukkan bukatu tare da na ’ya’yansu musamman a wannan lokaci na rashin kudi. Kuma ta bukaci matan su hada kai da mazajensu domin samun nasara a harkokinsu na rayuwa.
Hajiya Asma’u ta shawarci iyaye maza su kasance masu kula da tarbiyyar ’ya’yansu tare da sanya su a makaranta ta yadda za su kauce wa shiga cikin miyagun halaye da za su sanya kansu da iyayen cikin halin kaka-ni-ka-yi.
Ta yi nuni kan irin rawar da mata ke takawa a wajen tarbiyyantar da iyali amma ta ce hakan ba zai samun nasara ba sai da hadin kan maza a matsayinsu na jagororin iyali.
Sai ta yi kira ga matan da suka karanta aikin asibiti musamman a fannin haihuwa da sauran cututtukan mata su taimaka wa matan wajen duba su, maimakon barin maza likitoci na duba su.
Takardar ta ce Ma’aikatar Ilimi ta Jihar ta sanya sunan Uwargidan Gwamnan a makarantar sakandaren ’yan mata ta garin Kamba saboda irin gudunmawar da take ba da wa ga ilimin ’ya’ya mata a jihar.