Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe
Jimillar kuɗin tallafin ya kai Naira miliyan 14, wanda aka bayar domin taimaka wa al’umma
Uwargidan Sanata mai wakiltar Gombe ta Tsakiya, Hajiya Aminatu Danjuma Goje, ta raba wa mata da matasa 280 tallafin kuɗi na Naira 50,000 kowanne.
Jimillar kuɗin tallafin ya kai Naira miliyan 14, wanda aka bayar domin taimaka wa al’umma da ƙarfafa su wajen dogaro da kai.
- An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri
- Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu
Hajiya Hajjan Ubayo, wacce ta wakilci uwargidan Sanatan a wajen raba tallafin, ta bayyana cewa wannan tallafi na cikin shirye-shiryen da ake yi domin bunƙasa rayuwar mata da matasa a yankin.
Shugabar mata ta mazaɓar Gombe ta Tsakiya, Misis Rose Danjuma, ta yaba wa uwargidan Sanata Goje.
Ta ce irin wannan tallafi yana taimaka wa rayuwar jama’a da inganta yankin.
A makon da ya gabata, Sanata Danjuma Goje, ya raba Naira miliyan 200 ga mutum 2000, inda kowanne ya samu Naira 50,000.
Haka kuma, ya kawo kayan abinci da za a raba domin bikin Kirsimeti da Sabuwar Shekara.