Uwargidan Shugaban kasa ta bai wa marasa galihu tallafi a Nasarawa

Uwargidan Shugaban kasa Hajiya A’isha Muhammadu Buhari ta raba kayayyakin masarufi na miliyoyin Naira ga marasa galihu da suka hada da matan da suka rasa mazajensu da nakasassu da marayu a Jihar Nasarawa. A jawabin Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura wanda ya wakilci Hajiya A’isha Buhari ya ce Uwargidan Shugaban kasar ta ga ya dace […]

Uwargidan Shugaban kasa ta bai wa marasa galihu tallafi a Nasarawa
Uwargidan Shugaban kasa ta bai wa marasa galihu tallafi a Nasarawa

Uwargidan Shugaban kasa Hajiya A’isha Muhammadu Buhari ta raba kayayyakin masarufi na miliyoyin Naira ga marasa galihu da suka hada da matan da suka rasa mazajensu da nakasassu da marayu a Jihar Nasarawa.
A jawabin Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura wanda ya wakilci Hajiya A’isha Buhari ya ce Uwargidan Shugaban kasar ta ga ya dace ta tallafa wa marasa galihu ne a jihar musamman a wannan lokaci da ake fama da matsalar tattalin arziki da ya sa marasa galihu ba sa iya cin abinci sau uku a rana kuma ga shi ana azumi. Ya ce Hajiya A’isha Buhari ta umurce shi ya wakilce ta wajen rabon kayayyakin. Gwamna Umaru Al-Makura ya bukaci wadanda suka amfana da kayayyakin tallafin su tabbatar sun yi amfani da su yadda ya kamata, inda ya bukaci su ci gaba da bai wa gwamnatinsa da ta Buhari cikakken goyon baya domin ba su damar ci gaba da samar musu da ribar dimokuradiyya. Ya ce a nata bangaren gwamnatinsa ta bai wa wadannan mutane buhunan shinkafa da sauransu da kuma tsabar kudi a matsayin gudumawarta wanda ya bayyana a matsayin zakka.
Kayayyakin masarufin da Uwargidan Shugaban kasar ta bayar sun hadd da katan-katan na taliyar Indomi da makaroni da garin alkama da buhunan shinkafa da sauransu.
 An gudanar da taron raba kayayyakin ne a Dandalin Wasa na Lafiya fadar jihar.

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe

Iran da Amurka sun daidaita tattaunawar sulhu a Switzerland