Uwargidan Shugaban kasa ta tallafa wa wadanda harin bam ta ritsa da su a Yola

Uwargidan Shugaban kasa Hajiya A’isha Buhari ta kai agaji ga wadanda harin bam ya rutsa da su da suke kwance a asibitin tarayya (FMC) da ke Yola a Jihar Adamawa, tare da yi musu jaje. A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka kai harin bam din da misalin karfe bakwai da rabi na […]

Uwargidan Shugaban kasa ta tallafa wa wadanda harin bam ta ritsa da su a Yola
Uwargidan Shugaban kasa ta tallafa wa wadanda harin bam ta ritsa da su a Yola

Uwargidan Shugaban kasa Hajiya A’isha Buhari ta kai agaji ga wadanda harin bam ya rutsa da su da suke kwance a asibitin tarayya (FMC) da ke Yola a Jihar Adamawa, tare da yi musu jaje.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne aka kai harin bam din da misalin karfe bakwai da rabi na yamma, kuma Uwargidan Shugaban kasar ta bukaci kungiyoyin da ba na gwamnati ba su taimaka wa wadanda wannan masifar ta fada musu.
Uwargidan Shugaban kasar wadda Hajiya Zainab Nyako ta wakilta ta yi wa majinyatan fatar waraka da kuma yi musu addu’ar Allah Ya ba su lafiya wadanda kuma suka rasu Allah Ya yi musu rahama.
Babban Likitan Asibitin, Dokta Bala Sa’idu da kuma shugaban likitocin asibiti, Dokta Bemi Kala sun nuna godiyarsu ga Uwargidan Shugaban kasa kuma sun yi kira ga jama’a su taimaka wa wadanda suka ji rauni.
Wani wanda bam din ta rutsa da shi Malam Abdulkadir Muhammed ya mika godiyarsa a madadin wadanda suka samu rauni kan taimakon da aka ba su.