Uwargidan Tinubu ta ziyarci iyalan Lagbaja 

Marigayin ya rasu ya bar mata ɗaya da yara biyu.

Uwargidan Tinubu ta ziyarci iyalan Lagbaja 

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Babban Hafsan Sojin Ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, wanda ya rasu.

Ta samu rakiyar matar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Hajiya Nana Shettima, da matar Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Hajiya Ribadu.

Sun samu tarba mai kyau daga Uwargidan Shugaban Tsaron Kasa, Misis Oghogho Musa.

Sanata Tinubu ta yi addu’ar Allah Ya jiƙan marigayin, ta kuma rarrashin matar marigayin, Misis Mariya Abiodun Lagbaja.

“Allah ne kaɗai ya san okacin mutuwar mutum,” in ji uwargidan Tinubu.

A cewar mai ba ta shawara kan harkokin yaɗa labarai, Busola Kukoyi, Uwargidan Shugaban Ƙasa ta buƙaci iyalan mamacin da su ɗauki dangana.

Ta kuma ce gwamnati da al’ummar ƙasar nan ba za su manta da irin gudunmawar da Lagbaja ya bayar.

Da safiyar ranar Laraba ne, Gwamnatin Tarayya ta sanar da rasuwar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

Ya rasu a ranar Talata bayan ya sha fama da rashin lafiya.