Uwargidan Zulum ta raba wa nakasassu 400 tallafi a Borno

Uwargidan Gwamnan Borno, Dokta Falmata Babagana Umara Zulum tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Mata ta Jihar Borno sun ƙaddamar da rabon kayayyaki ga nakasassu albarkacin Ranar Masu Buƙata ta Musamman ta Duniya. An gudanar da rabon kayayyakin ne a babban ɗakin taron Fadar Gwamnatin Borno da ke Maiduguri. Jirgin mataimakin Zulum ya kama da wuta […]

Uwargidan Zulum ta raba wa nakasassu 400 tallafi a Borno

Uwargidan Gwamnan Borno, Dokta Falmata Babagana Umara Zulum tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Mata ta Jihar Borno sun ƙaddamar da rabon kayayyaki ga nakasassu albarkacin Ranar Masu Buƙata ta Musamman ta Duniya.

An gudanar da rabon kayayyakin ne a babban ɗakin taron Fadar Gwamnatin Borno da ke Maiduguri.

Aminiya ta ruwaito cewa uwargidan Gwamnan ta raba kayan tallafin ga nakasassu 400 da suka haɗa da matasa maza da mata da yara.

Bayanai sun ce daga cikin kayayyakin da uwargidan Gwamnan ta raba sun haɗa da kekunan ɗinki 100, injin niƙa 40, kayan alfarma 200, da suka kunshi turaren wuta, da tallafin kuɗi na Naira dubu goma-goma ga mutum 60.

Ta ce an yi wannan yunƙurin ne domin inganta rayuwa da ’yancin nakasassu da masu buƙata ta musamman a jihar.

Da take jawabin maraba, Kwamishinar Mata da Ci gaban Jama’a ta jihar, Zuwaira Gambo, ta jaddada ƙudirin gwamnatin wajen sadaukar da kai da tallafa wa nakasassu tana mai jinjina wa irin jagorancin da jihar ke da shi ƙarƙashin Gwamna Babagana Zulum.

Wasu jiga-jigan ƙungiyoyin nakasassu waɗanda suka halarci taron sun bayyana godiyar su bisa wannan karamci na Gwamnatin Borno kan ƙoƙarin da take yi na inganta rayuwar mambobinsu.

Wasu daga cikin waɗanda suka ribatu da tallafin sun bayyana jin dadinsu yayin da suke gode wa Kwamishinar da kuma ma’aikatar bisa gagarumin tallafin da suka bayar.

A nasa jawabin, Babban Sakataren Ma’aikatar Mata da Ci gaban al’umma, Alhaji Mohammed Hamza, ya yaba wa masu ruwa da tsaki na jihar bisa ƙoƙarin tare da bayyana kwarin guiwar cewa tallafin zai ƙara inganta rayuwar nakasassu a Jihar Borno.