Valencia ta dauki Edinson Cavani
Cavani yana filin Mestella a wasan da Atletico Madrid ta lallasa Valencia.
Dan wasan kasar Uruguay Edinson Cavani, ya sanya hannu a kwantiragin shekara biyu da kungiyar Valencia.
Cavani mai shekara 35 bai samu kungiya ba tun bayan da kwantiraginsa ya kare da Manchester United a karshen kakar wasan da ta gabata.
- “Yadda Nake Yin Saka Duk Da Larurar Rashin Gani”
- Bayan ‘tuban’ Bello Turji, ’yan bindigar Zamfara sun fara komawa dajin Birnin Gwari
A baya, dan wasan gaban ya taba buga wa Paris Saint Germain, Napoli da Palermo.
Cavani na filin wasan Valencia na Mestalla a lokacin da Atletico Madrid ta lallasa kungiyar da ci 1-0 a ranar Litinin a gasar La Liga.
Kungiyar ta yi nasarar lashe wasa daya ne cikin wasanninta uku na farko.