Van Dijk ya kafa tarihin buga wasa na 100 a gasar Premier
Kyaftin ɗin kasar Netherlands ya samu maki 262 a wasa 100 a gasar Premier a Anfield.
Ɗan wasan Ƙungiyar Liverpool kuma ɗan kasar Netherlands, Virgil van Dijk ya kafa tarihin buga wasa 100 a gasar Premier ta Ingila a wasan da Liverpool ta doke Brentford 2-0 a filin wasa na Anfield ranar Lahadin da ta gabata.
A cikin wasannin da ya buga ƙungiyar ta samu nasara a wasa 82 a gida da canjaras 16, yayin da aka yi rashin nasara a kanta sau biyu.
- Aro: Sterling ya tafi Arsenal, Chelsea ta ɗauko Sancho
- Abubuwan da ya kamata ku sani game da cutar ƙyandar biri
Van Dijk ya fafata a wasan da aka ci Liverpool a Anfield inda Leeds United ta lallasa su da ci 2-0 a kakar 2022/2023, sai wasan Crystal Palace ta doke Liverpool a Anfield da ci daya mai ban haushe a kakar bara.
Kyaftin ɗin kasar Netherlands ya samu maki 262 a wasa 100 a gasar Premier a Anfield, wanda ke gabansa shi ne Patrice Evra mai maki 263 a Manchester United a Old Trafford.
Van Dijk tsohon dan kwallon Kungiyar FC Groningen da Celtic da Southampton ya koma Liverpool a ranar 1 ga Janairun 2018, kuma kwantiraginsa zai ƙare a ƙarshen kakar bana a Anfield.
Liverpool ta fara wasan bana da doke Ipwich Town da ci 2-0 a ranar 17 ga Agusta a wasan makon farko.
A karon farko Liverpool ta buga wasa a Anfield ba tare da kocinta Jurgen Klopp ba wanda ya yi murabus a kakar da ta gabata, bayan shekara tara yana jan ragamarta.
A wannan Lahadin Liverpool za ta je gidan Manchester United don buga wasan mako na uku a ƙarƙashin sabon kocinta Arne Slot.