Varayi sama da 150 sun tuba a yankin Lere
Varayi da masu sayen kayan sata sama da 150 ne suka tuba tare da miqa makamansu a garin Unguwar Bawa da ke Qaramar Hukumar Lere a Jihar Kaduna a qarshen makon jiya. Yayin tubar an gudanar da wani taro, inda varayin suka riqa fitowa xaya-bayan-xaya, suna bayyana sunayensu da irin abubuwan da suke aikata a […]

Varayi da masu sayen kayan sata sama da 150 ne suka tuba tare da miqa makamansu a garin Unguwar Bawa da ke Qaramar Hukumar Lere a Jihar Kaduna a qarshen makon jiya.
Yayin tubar an gudanar da wani taro, inda varayin suka riqa fitowa xaya-bayan-xaya, suna bayyana sunayensu da irin abubuwan da suke aikata a baya da kuma yin rantsuwa da Alqur’ani Mai girma ga Musulmi da kuma rantsuwa da Littafin Baibul ga Kiristoci cewa har abada sun tuba, ba za su sake yin sata ba.
Da yake jawabi a wajen taron Kwamandan Rundunar ’Yan sanda ta ShiyYar Kafanchan wanda kuma ya jagoranci taron, Mista Kayode Sunday ya ce wannan abu da waxannan mutane suka yi na tuba daga aikata miyagun ayyukan da suke yi a da, abu ne da ake yi yanzu a duk faxin Najeriya.
Ya ce yanzu mutane da dama suna miqa makamansu ga jami’an tsaro suna ba da gudunmawa wajen yaqar miyagun ayyuka a Najeriya.
“Kamar yadda kuka yi rantsuwa da littafai masu tsarki cewa kun daina sace-sace da miyagun ayyuka, muna fata za ku yi aiki da wannan rantsuwa da kuka yi. Kuma muna kira ga dukan waxanda suke riqe da makamai suke aikata miyagun ayyuka a Najeriya, su yi qoqari su tuba su miqa makamansu,” inji shi.
A jawabin Kantomar Qaramar Hukumar Lere, Misis Laraba Kantoma ta ce ganin halin da aka shiga a qaramar hukumar na sace-sace da fashi da garkuwa da mutane ya sanya aka samu waxansu mutane, suka yi qoqarin kafa qungiyar sa-kai domin yaqar waxannan munanan al’amura. Don haka ta yaba wa qungiyar kan qoqarin da take yi wajen magance waxannan munanan ayyuka a yankin.
Kantomar wadda Mataimakin Daraktan Sashin Jin Daxi da Walwalar Jama’a na Qaramar Hukumar, Alhaji Munkaila Muhammad Galadima ya wakilta, ta yi kira ga waxanda suka tuban su yi qoqari su kama sana’o’in da doka ta yarda a yi.
Tun farko a jawabin Shugaban Qungiyar Sa-kai ta yaqi da varayi da masu garkuwa da mutane da ake kira ’Yan Bula, Alhaji Musa Babawuro, ya ce mutane sama da 150 da suka qunshi manyan varayi da varayin shanu da awaki da masu fasa shaguna da masu sayen kayayyakin sata dukansu sun tuba, kuma masu makamai daga cikinsu sun miqa makamansu.
Ya ce daga lokacin da suka fara gudanar da ayyukansu a yankunan qananan hukumomin Lere da Kauru da Kubau da ke Jihar Kaduna da Qaramar Hukumar Doguwa da ke Jihar Kano zuwa yanzu sun tubar da varayi sama da 1800.
Ya miqa godiyarsu ga Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna kan goyon baya da haxin kan da yake ba su don gudanar da ayyukansu na yaqi da varayi da masu garkuwa da mutane.
Waxansu daga cikin masu tubar da jaridar Aminiya ta zanta da su, sun ce sun tuba ne tsakani da Allah kuma da yardar Allah ba za su sake komawa ga waxannan munanan ayyuka ba.