Venezuela ta sanar da ficewa daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya
Venezuela na ganin ICC na nuna wariya ta fuskar yankuna, inda take zargin kotun da nuna son kai wajen gudanar da aikinta.
Gwamnatin Venezuela ta sanar da cewa za ta fice daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC), tana mai zargin kotun da nuna son kai wajen gudanar da aikinta.
Ministan Harkokin Wajen ƙasar, Felix Plasencia, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ya ce tuni gwamnatin ta sanar da Majalisar Ɗinkin Duniya matakinta na “ƙarshe kuma wanda ba za a sauya ba” na ficewa daga kotun.
- Wani boka ya yi iƙirarin zai ba Gwamnan Sakkwato nasara a Zaɓen 2027
- An yi jana’izar manoma 26 da aka kashe a harin ’yan bindiga a Zamfara
Plasencia ya ce shugabar riƙon ƙwarya ta ƙasar, Delcy Rodríguez, ce ta bayar da umarnin ɗaukar wannan mataki, bayan da ta karɓi ragamar mulki a watan Janairu bayan hambarar da tsohon shugaban ƙasar, Nicolas Maduro.
Ya ce Venezuela na ganin Kotun ICC na nuna wariya ta fuskar yankuna, inda ta fi mayar da hankali kan ƙasashen Afirka da Latin Amurka fiye da sauran sassan duniya.
Sai dai kotun mai hedikwata a birnin Hague na ƙasar Netherlands ta ce har yanzu ba ta karɓi sanarwar ficewar Venezuela a hukumance ba.
Kotun ta bayyana cewa tana takaicin duk wata ƙasa da ta yanke shawarar ficewa daga haɗin gwiwar da aka kafa domin hukunta masu aikata manyan laifukan ƙasa da ƙasa.
Ta kuma bayyana cewa ficewar ƙasa daga ICC ba ta fara aiki sai bayan shekara guda da gabatar da sanarwar a hukumance.
Kotun ta ƙara da cewa ko bayan ficewar, Venezuela za ta ci gaba da kasancewa ƙarƙashin nauyin haɗin gwiwa a bincike da shari’o’in da aka fara tun tana mamba a kotun.
A halin yanzu, ICC na gudanar da bincike kan zarge-zargen aikata laifukan cin zarafin bil’adama da ake zargin an aikata a lokacin murƙushe masu zanga-zanga a Venezuela tun daga shekarar 2014.
A watan Disamban 2025, Majalisar Dokokin Venezuela ta fara matakan soke yarjejeniyar Rome Statute, wadda ita ce ta kafa Kotun ICC, bayan da kotun ta rufe ofishinta da ke Caracas saboda rashin cimma matsaya da gwamnatin ƙasar.
Haka kuma, a watan Maris na wannan shekara, ICC ta yi watsi da ƙarar da Venezuela ta shigar, wadda ke zargin takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba mata ya kai matsayin laifukan cin zarafin bil’adama.
Sanarwar ficewar Venezuela ta zo ne a ranar da ƙasashe mambobin ICC suka amince da tsige babban mai gabatar da ƙara na kotun, Karim Khan, bisa zargin cin zarafin mata ta hanyar lalata.
Sai dai Khan ya musanta zargin, yayin da lauyoyinsa suka bayyana cewa zai ƙalubalanci matakin korarsa.
A shekarar 2024, Khan ya nemi kotun ta bayar da sammacin kama Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, da tsohon Ministan Tsaron ƙasar, Yoav Gallant, bisa zargin aikata laifukan yaƙi da kuma laifukan cin zarafin bil’adama a Zirin Gaza.
Bayan Donald Trump ya koma kan mulkin Amurka a karo na biyu a shekarar 2025, gwamnatin Amurka ta ƙaƙaba wa Kotun ICC da wasu alƙalanta takunkumi.
Amurka da Isra’ila ba sa cikin ƙasashen da suka amince da zama mambobin Kotun ICC, wadda ke shari’ar mutanen da ake zargi da aikata manyan laifukan ƙasa da ƙasa, ciki har da laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil’adama.