Victor Boniface ya yi hatsarin mota a Jamus

Dan wasan gaban Nijeriya da kungiyar kwallom kafa ta Leverkusen, Victor Boniface ya yi hatsarin mota a ƙasar Jamus

Victor Boniface ya yi hatsarin mota a Jamus
Victor Boniface ya yi hatsarin mota a Jamus

Dan wasan gaban Nijeriya da kungiyar kwallom kafa ta Leverkusen, Victor Boniface ya yi hatsarin mota a ƙasar Jamus.

Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Lahadi, inda ɗan wasan ya yi taho mu gama da wata babbar mota, wanda hakan ya sa aka garzaya da shi asibiti.

Ɗan wasan mai shekara 23 ya taimaka wa Leverkusen da ƙwallo wajen doke Eintracht Frankfurt a ranar Asabar.

Boniface ya wallafa bidiyon yadda motarsa ta lalace a Instagram.

Bidiyon ya nuna yadda daya daga cikin hannunsa ke zubar da jini.

A bidiyon an yadda motar dan wasan ta lalace sosai sakamakon karon da ta yi da wata babbar mota.

Rahotanni sun bayyana cewar hatsarin ya faru ne lokacin da ɗan wasan yake kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama na Frankfurt da safiyar ranar Lahadi.