Virgin Atlantic zai fara jigila daga London zuwa Legas

Kamfanin jiragen sama na Virgin Atlantic ya ce zai dawo da jigilar fasinja daga birnin London da kasar Birtaniya zuwa Legas a Najeriya. Sanawar kamfanin a safiyar Asabar ta ce zai fara jigila daga ranar 10 ga Satumba, 2020 daga filin jirgi na Heathrow, da sabon jirgin A350-1000, wata biyar da dakatar da zirga-zirga kasa […]

Virgin Atlantic zai fara jigila daga London zuwa Legas

Kamfanin jiragen sama na Virgin Atlantic ya ce zai dawo da jigilar fasinja daga birnin London da kasar Birtaniya zuwa Legas a Najeriya.

Sanawar kamfanin a safiyar Asabar ta ce zai fara jigila daga ranar 10 ga Satumba, 2020 daga filin jirgi na Heathrow, da sabon jirgin A350-1000, wata biyar da dakatar da zirga-zirga kasa da kasa a Najeriya.

“Za a ba kowane fasinja kayan kariyar lafiya da suka hada da takunkumi uku da za su yi amfani da su a sararin samaniya, man wanke hannu da kuma kyallen goge-goge”, inji sanarwar.

A baya ya so dawo da jigilar fasinjoji tsakanin biranen biyu daga ranar 25 ga wata Agusta, amma Najeriya ba za ta bude sufurin jiragen sama na kasa da kasa ba sai ranar 29 ga watan August.

Kamfanin ya ce an samar da sabbin kirkire-kirkiren fasaha a jirgin da zai fara jigila tsakanin biranen domin tabbatar da kare lafiyar matafiya a daga filin har a sararin samaniya.

Matakan sun hada da cikakken tsafta da feshin magani na musamman a dukkannin kofofin shiga filin zauren jiran jirgi da wuraren tantance fasinjoji da ma a kujerun jirgi da ban dakinsa kafin kowace tafiya.

Sanarwar dauke da sa hannun Manajar Kasuwancin Virgin Atlantic, Justin Bell, ta ce, “Mun bayar da muhimmanci ga lafiya da walwalar matafiya da ma’akata, ta hanyar tabbatar ta tazara a filin jirgi da kuma cikakken tsaftace cikin jirage. Za kuma mu ba kowane matafiyi jakar kula da lafiiya”.