Wa ke son haifar da rudu a Majalisar Dokokin Jihar Katsina?

Jihar Katsina, tun daga kafuwarta a 1987 har zuwa yau, tana daya daga cikin jihohin da aka rika samun zaman lafiya da kwanciyar hankali ta fannonin rayuwa da dama, kamar ta bangaren addini, kabilu, bangare da kuma a siyasance. Sai dai kuma abin takaici da al’ajabi, wasu sun dukufa wajen ganin sun haifar da rudu […]

Wa ke son haifar da rudu a Majalisar Dokokin Jihar Katsina?
Wa ke son haifar da rudu a Majalisar Dokokin Jihar Katsina?

Jihar Katsina, tun daga kafuwarta a 1987 har zuwa yau, tana daya daga cikin jihohin da aka rika samun zaman lafiya da kwanciyar hankali ta fannonin rayuwa da dama, kamar ta bangaren addini, kabilu, bangare da kuma a siyasance. Sai dai kuma abin takaici da al’ajabi, wasu sun dukufa wajen ganin sun haifar da rudu da fitina a tsakanin al’ummar jihar nan, don haka suka zabi su fara kunna gaba da kiyayya da rashin jituwa a Majalisar Dokokin jihar, duk da cewa an samu sabuwar gwamnati, bisa jagorancin sabon gwamna, wanda kowa ke masa kyakkyawan zato da tsammanin adalci.

Ina mamakin yadda wani mutum da ya kira kansa dan jarida yake ta fadi-tashi, yake ta kwarmato da tsugudidi da gutsuri-tsoma, wajen ganin ya bata wa gwamnatin Masari suna, kamar kuma yadda ya dukufa wajen kware wa sabo kuma zababben Shugaban Majalisar Dokoki, Hon. Aliyu Maduru zani a kasuwa.
Hankalina ya dauku ga wani rahoton kanzon kurege, da wani dan rahoto mai suna danjuma Katsina ya rubuta, wanda aka buga a jaridar Almizan, ta ranar Juma’a, 10 ga Ramadan, 1436 BH, shafi na 16, wanda babu komai cikinsa sai bakar aniyar haddasa fitina ga al’ummar Jihar Katsina.
Kamar yadda kanun rahoton yake: “An nuna damuwa kan yadda Izala ta mamaye Majalisar Dokokin Jihar Katsina,” tun daga nan mutum zai tsinkayi inda aka nufa, cewa ba alheri ake tunkarar al’ummar Katsina da shi ba. dan jaridar ya ruwaito Malam Yakubu Yahaya, wakilin ’yan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky, a jawabinsa wai yana nuna damuwa da yadda ’yan Majalisar Dokokin Jihar Katsina ’yan Izala suka mamaye majalisar, har ma ya tsakuro malamin yana cewa: “A da muna hulda da wasu ’yan siyasa ne, wadanda suke tunanin ra’ayin jama’a da tsoron fushinsu. Amma yanzu za mu fuskanci dalibai ne na wata akidar da suke ganin su kadai ne Musulmi. Duk wanda bai tare da su kafiri ne.”
Ni kuwa na ce, indai har malamin ya fadi haka, to babu dalilin da zai sa ya yi wannan batu, domin kuwa a bayyane yake cewa su ’yan uwa mabiya Zakzaky babu ruwansu da siyasa irin ta dimokuradiyya. Sun sha nanata cewa gwamnati irin wannan ta dagutu ce, don haka ba za su shiga cikinta ba. An samu bayani da hujjoji karara cewa ba su shiga cikin harkar zabe ba da ya wuce. Ma’ana, ba su tsaida kowa takara ba, ba su yanki katin rijista ba kamar sauran ’yan kasa kuma ba su kada kuri’a ba. Don haka, me ya sa kuma bayan an kafa gwamnati za su nuna damuwa da wadanda suka shiga zabe kuma al’umma suka zabe su? Don haka wannan korafin bai da dalili kuma ba su ya kamata su yi korafi ba.
Kamar yadda mai rahoton ya rubuta, wai bincikensa ya gano cewa cikin ’yan majalisa 34, 23 har da shugaban majalisar ’yan Izala ne. Kamar rahoton ya ce: “Bincike ya gano cewa Izala sun karfafa ma ’ya’yansu su shiga kuma su yi takara a APC, yayin da ’yan siyasa suka rika daukar cewa jam’iyyar ba za ta kai labari ba, sai kuma guguwar canji ta taho.” Abin tambaya a nan shi ne, wane ne ya zabi wadannan ’yan Majalisa 34 daga sassa daban-daban na jihar? A karkashin wace jam’iyya ko jam’iyyu aka zabo su? Wane tsarin mulki ne ya kawo su wannan majalisa? Shi kuma Shugaban Majalisar, wa ya zabe shi kuma wane tsari aka bi wajen zabensa?
A iya sani na, talakawan Jihar Katsina ne suka zabo wadannan ’yan majalisa daga kananan hukumomi 34 na jihar. An zabo su ne daga jam’iyyu daban-daban, musamman APC da PDP da dokar kasa ta kafa su kuma ta amince masu su shiga zabe. ’Yan majalisar ba su shiga zabe da sunan wani addini ko wata akida ta Izala, darika ko Shi’a ba, an zabo su ne kawai a matsayinsu na ’yan Najeriya, ’yan Jihar Katsina da suka cancanci wakiltar al’ummarsu ba tare da wariya ko nuna bambancin addini, yare ko bangare ba. Ya kamata mai korafin nan ya fahimta da cewa Tsarin Mulkin kasa ne ya bayar da hurumin zabarsu bisa mulkin dimokuradiyya. Su kuma ’yan kungiyar ’yan uwa sun ce ba su amince da tsarin siyasar ba. Mai korafin cewa wai ’yan Izala sun mamaye majalisar, to me ya hana lokacin da aka zo zabe, su ma su tsayar da nasu ’yan takarar? Shin sun tsayar da nasu ne aka ki zabensu? Batun ngaskiya shi ne, ba su tsayar da kowa ba kuma ba su ma fita zaben ba. To idan wani ya tsaya kuma ya ci zabe, sai a ce don me ya mamaye wuri? Kuma ai duk wanda aka zaba don rike mulki a kasar nan, da Kundin Tsarin Mulkin kasa zai yi aiki, ba da kundin tsarin mulkin wata kungiyar addini ba. Ka ga ke nan wata kungiyar addini ba ta da hujjar yin kukan wata kungiya ta mamaye ta.
A zargin mai rahoton cewa wai an take doka da cancanta, aka zabi shugaban majalisa. Ina hujjar wannan zargi? A rahoton fa an ce wakilai 23 ne suka rinjayi 34, to ko a ina, ai 23 sun rinjayi 34 kuma sun isa su zabi shugaba kuma a amince, domin kuwa haka ka’idar dimokuradiyya take, mai yawa shi ke da mulki. Don haka ina kalubalantar mai zargin nan ya bincika, tun da aka fara dimokuradiyya a 1999 zuwa yau, babu lokacin da aka yi sahihin zaben Shugaban Majlisa a Jihar Katsina mafi tsafta da bin ka’ida kamar wannan lokacin.
Abin da ya kara bata mani rai da rahoton nan shi ne, babu inda dan jaridar ya tuntubi mutanen da suka kamata domin jin ta bakinsu. Hatta shi kansa Malam Yakub, an ari bakinsa ne aka ruwaito abin da ya fada a wurin taro, ba wai dan jaridar ne ya nemi bayani kai tsaye daga wurinsa ba. Su kuma bangaren Sufaye, dan jaridar bai tuntube su ba, sai kawai ya ari bakinsu ya ci musu albasa.
Kamar yadda ya ce wai bangaren Sufaye sun yi taro wai za su kai wa gwamna ziyara, inda wai za su jawo hankalinsa don kada ya fifita wata kungiyar addini. Ya kamata dan rahoton nan ya gane cewa Gwamna Masari na kowa ne, babu ruwansa da bambancin akida ko addini. Shi gwamnan al’ummar Jihar Katsina ne, babba da yaro, mace da namiji, yaro da babba, Kirista da Musulmi, dan Izala ko dan darika ko dan Shi’a. Shin ko kungiyar ’yan nuwa ta taba gayyatar Masari wani taro bai je ba, ko kuwa sun taba kai masa ziyara kan wani abu bai amsa ba?
Shin wai me ya sa danjuma Katsina ya zabi shafa wa gwamnatin Masari kashin kaji, me ya sa ya zabi ya rika kirkira rahoton karya da nufin hada husuma da haifar wa al’umma rashin jituwa? Idan ba zan manta ba, ya taba rubuta wani ra’ayi shigen wannan a jaridar Aminiya ta ranar Juma’a 19 ga Yuni, 2015. Ni dai ina jawo hankalinsa kuma ina yi masa nasiha da ya ji tsoron Allah. Idan ba zai rubuta alheri ba, to ya guji rubuta abin da zai kawo tashin hankali tsakanin al’umma, domin kuwa Allah Ya la’anci mai tayar da fitina, domin idan ta zo, za ta shafi mai ruwa da ma wanda bai da ruwa a ciki.
Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya a jiharmu da kasarmu baki daya, amin!
Muhammadu Mustapha (08058538165), ya rubuto daga Mani, Jihar Katsina

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna