Wa ya babbake kaninsa kan satar N4,500 a jihar Nasarawa
Ana zargin wani mutum mai suna Iliya Iliya mai inkiyar ‘Tractor’ da wasu abokanansa da laifin babbake dan uwansa, Alkasim Iliya mai inkiyar ‘Popping’ kan zargin satar naira dubu hudu da dari biyar a garin Maura na jihar Nasarawa. Majiyar da ta tabbatarwa Aminiya faruwar lamarin ta ce, Iliya wa ne ga Alkasim kuma mahaifinsu […]
Ana zargin wani mutum mai suna Iliya Iliya mai inkiyar ‘Tractor’ da wasu abokanansa da laifin babbake dan uwansa, Alkasim Iliya mai inkiyar ‘Popping’ kan zargin satar naira dubu hudu da dari biyar a garin Maura na jihar Nasarawa.
Majiyar da ta tabbatarwa Aminiya faruwar lamarin ta ce, Iliya wa ne ga Alkasim kuma mahaifinsu daya sai dai kowanensu mahaifiyarsa daban.
- Uwa ta rataye ’ya’yanta 2 don ta yi lalata da kare
- Ya rayu shekara 53 da kudin karfe a cikin hancinsa
A cewar majiyar, lamarin ya faru ne a unguwar Tudun Adabu na Karamar Hukumar Obi ta jihar Nasarawa, inda Iliya da abokanansa suka zargi Alkasim da satar kudin wanda a dalilin haka suka daure shi da igiya kuma suka kwarara masa man fetur sannan suka cinna masa wuta.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, ASP Rahman Nansel, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa tuni an kama Iliya kuma za a ci gaba da bincike domin ganin sauran ababen zargin sun shiga hannu.
Shugaban Karamar Hukumar, Muhammad Oyigye Iyamoga, ya kiraye al’ummarsa da su guji daukar doka a hannunsa tare da gargadi a kan kaurace wa duk wani lamari da zai tayar da zaune tsaye a yankin.