Wa ya fi mugunta tsakanin mai gona da mai kankana?
Wadansu mutum biyu makwabtan juna a gona. Daya ya noma kankana ta yi kyau, sai makwabcinsa ya ce ya yaba ta kuma ya kamata ya tsinke ta ya kai kasuwa. Mai kankana ya ce haka za a yi. To amma sai ya tuna makwabcinsa mugu ne, don haka ya yi sammako zuwa gonar ya haye […]
Wadansu mutum biyu makwabtan juna a gona. Daya ya noma kankana ta yi kyau, sai makwabcinsa ya ce ya yaba ta kuma ya kamata ya tsinke ta ya kai kasuwa. Mai kankana ya ce haka za a yi. To amma sai ya tuna makwabcinsa mugu ne, don haka ya yi sammako zuwa gonar ya haye bishiya. Can sai kuwa ga makwabcin ya zo da adda, ya sanya addar duk ya daddatsa kankanar bibbiyu, makwabcin nan yana kallonsa bai ce kala ba balle ya hana shi, sai ya rage biyar kacal. Ya juya zai tafi mai kankanar ya ce ai da ka tsaya ka karasa abin da ka fara. Ashe mai kanana da abin da yake zuciyarsa, sai ya kai kara ga alkali, aka yi diyyar kudin kankana mai gona ba ya da su, sai aka amshe gonar aka mika wa mai kankana. To a cikin mutanen nan biyu, wanne ya fi mugunta, wanda ya ga za a yi masa barna ya bari sai da aka gama don ya raba makwabcinsa da gona ko kuwa wanda ya yi barnar don raba makwabcinsa da kankanarsa?
Wanda ya amshe gona ya fi mugunta – Falalu Gugar Karfe
Daga Ahmad Kabir S/Kuka, Katsina
Falalu Gugar Karfe: Ai wannan maganar ma ba sai an je ko’ina ba, wanda ya sa aka ƙwace gona aka ba shi ya fi wancan mai yi masa ɓarna mugunta. Yana fa kallonsa yana aikata masa ba daidai ba, amma saboda tsabar ƙeta da mugunta ya yi shiru ya ƙyale shi, domin ya san ƙarshen abin ke nan. Kuma wai har ya ce masa ya iyar da abin da yake yi saboda ya san abin da ya ƙulla a ransa. Ƙila ma tuni yake tunanin hanyar mallake gonar bai samu ba sai a yanzu. Amma don kawai abokin ya zo yana sarar kankanar shi ke nan, ai akwai yiwuwar ba ya cikin hankalinsa a lokacin da yake sarar.
Mai karɓar gona ne ke da magunta – Labaran Mai Nama
Daga Ahmad Kabir S/Kuka, Katsina
Labaran Mai Nama: Mai mugunta bayan mai karɓar gona yake. Shi mai sare kankana a iya cewa baƙin ciki ne kawai ba mugunta ba, amma ka amshe mini gona bayan ƙila ko kuɗi aka yi wa ɓarnar da na yi maka ko kusa ba za su kai koda rabin kudin gonar ba. Kuma ai yana iya sanya wata ko ya ce sai ya sake noma masa wata,amma sai a yi ƙoƙi-ƙurmus? Yau ai ba shi kaɗai ya kashe ba, duk iyalan ya yi wa. Yau in babu gona ai babu abinci. Gaskiya mai ƙwace gona ya fi mugunta wadda kuma ba a kan mutun ɗaya ba, hatta ma da wasu halittun ya yi masu mugunta.
Mai gonar kankana ne mugu – Auwal Abdullahi
Daga Abbas Dalibi, Legas
Auwal Abdullahi: A gaskiya ni a ra’ayina, mai gonar kankana ne ya fi mugunta saboda ya kamata ya hana makwabcinsa lalata kankanar, tun da ya gan shi amma sai ya bar shi har sai da ya gama bata ta sannan ya yi kararsa, aka hukunta shi. Ai ka ga ya fi mugunta ke nan.
Mai kankana ya tabbata mugu – Abubakar Bala
Daga Abbas Dalibi, Legas
Abubakar Bala: Mai gonar kankana ya fi mugunta, domin yana kallo lokacin da makwabcinsa ya shiga gonar ya fara barna amma bai dakatar da shi ba. Wannan ya tabbatar da cewa shi ne ya fi makwabcin nasa iya mugunta saboda ya kyale shi sai da ya gama iya barnar da zai iya sannan ya maka shi a gaban kuliya. Ka ga wannan ai shi ne ya san kan mugunta.
Mai gonar kankana ya fi mugunta – Ibrahim Umar
Daga Aliyu Babankarfi, Zariya
Ibrahim Umar: Wanda aka bata wa gonar kankana ya fi mugunta. Shi wanda ya fasa kankana ya yi ne domin bakin ciki, amma shi mai gonar kankana tsabar mugunta ce, saboda ya san ba ya da asara, tunda wanda ya fasa mai kankana shi ma yana da gonar da ta fi tasa. Don haka mai gonar kankana shi ne mugu.
Wanda aka fasa wa kankana ya fi mugunta – Buhari Ibrahim
Daga Aliyu Babankarfi, Zariya
Buhari Ibrahim: A ra’ayina, mai gonar kankana ya fi mugunta, dalili shi ne watakila gonar mai fasa kankanar ta fi ta mai gonar kankanar yabanya, don haka ya sa yana kallo ana yi masa barna bai yi magana ba, don ya san cewa gonar wancan za ta zama tashi. Don haka mai gonar kankana ya fi mugunta.