Wa ya kashe ƙaninsa kan ‘sholisho’ a Bauchi
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan uwan junan sun sha yin faɗa da makamai.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wani matashi mai shekara 30, bisa zargin kashe ƙaninsa har lahira, ta hanyar daɓa masa wuka.
Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Ahmed Wakil ne, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Bauchi.
- Hajji: Gwamnatin Jigawa ta bai wa kowane maniyyaci kyautar miliyan ɗaya
- Sojoji sun hallaka ’yan bindiga 11 a Katsina da Zamfara
Ya ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da aka kai wa rundunar.
“An garzaya da wanda aka daɓa wa wuƙar zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Ɓalewa (ATBUTH), amma likita ya tabbatar da mutuwarsa.
“Bayan faruwar lamarin ’yan sanda suka fara farautar wanda ake zargin, sannan aka kama shi a kusa da unguwar Kasuwan Shanu a Bauchi.
“Binciken da ’yan sandan suka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya daba wa ƙaninsa wuka a ranar 31 ga watan Maris 2024 da misalin ƙarfe 4 na asuba bayan saɓani ya barke a tsakaninsu,” in ji shi.
Wakil, ya ƙara da cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da yayan ya hana ƙaninsa shan kayan maye (sholi) a ɗakinsu.
“Hakan ta sanya suka fara faɗa da juna. Jim kaɗan bayan sulhunta su, wanda ake zargin ya ɗauko wani abu mai kaifi, wanda ake zargin wuƙa ce, ya daɓa wa ƙanin nasa.
“Bincike ya nuna ’yan uwan junan sun jima suna faɗa da juna ta hanyar amfani da muggan makamai,” in ji shi.
Wakil, ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Auwal Musa, ya bayar da umarnin gudanar da bincike a kan lamarin kafin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya.