Wa ya sanya Gwamnonin G-7 a tsaka mai wuya?

G-7 shi ne takaitaccen sunan da ’yan jarida suka sanya wa gwamnonin PDP bakwai da suka raba ta gida biyu, saboda kamar yadda suka ce suna yunkurin tabbatar da gaskiya a cikin PDP, kuma ta rika tafiya a doron manufofin da iyayenta suka dorata a kai. G-7 su ne Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido da […]

Wa ya sanya Gwamnonin G-7 a tsaka mai wuya?
Wa ya sanya Gwamnonin G-7 a tsaka mai wuya?

G-7 shi ne takaitaccen sunan da ’yan jarida suka sanya wa gwamnonin PDP bakwai da suka raba ta gida biyu, saboda kamar yadda suka ce suna yunkurin tabbatar da gaskiya a cikin PDP, kuma ta rika tafiya a doron manufofin da iyayenta suka dorata a kai.

G-7 su ne Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido da na Kano Rabi’u Kwankwaso da na Sakkwato Aliyu Magatakarda Wammako da na Neja Babangida Aliyu da na Adamawa Murtala Nyako da na Kwara Abdulfatah Ahmed, sai baren cikinsu Rotimi Ameachi na Ribas.
Dukansu in ban da Gwamnan Kwara a shekara ta 2015 za su bar kujerunsu saboda wa’adin mulkinsu ya cika. Wasunsu za su iya neman wasu mukamai kamar Shugaban kasa ko Sanata ko su yiwo kasa su nemi Majalisar Tarayya. In kuma ba haka ba su dauki wani layin dan takarar Shugabancin kasa la’alla in aka kafa gwamnati su samu dafa wani iko.
Sule Lamido ya sha fada cewa bukatun da suke da shi a cikin wannan rigima guda biyar ne. Na farko, a mayar wa Baba Maimangwaro shugabancin PDP da ya kafa, na biyu a dage dakatarwar da aka yi wa Gwamna Rotimi Ameachi, na uku, a sauke Bamanga Tukur daga shugabancin jam’iyyar ta kasa, na hudu a sake sabon taron kasa na jam’iyyar, na biyar a rika gudanar da jam’iyya a bisa dokokinta.
Idan Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yarda da wadannan bukatu kuma ya zartar da su, za a zauna lafiya kowa zai maida wukarsa. In kuma ba haka ba, Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Kwankwaso ya ce ko dai G-7 su tattare su koma APC ko su shiga wata karamar jam’iyya da ba ta kai APC ba su raya ta, ko kuma su bullo da wata sabuwa kar, su bar PDP.
A yadda na fahimci wannan yanayi da Jam’iyyar PDP ta fada, wadannan gwamnoni suna cikin tsaka mai wuya, kowane mataki suka dauka. In sun yi sulhu ba su tsira ba, imma ba su yi ba ba su tsira ba. Za a iya daukar halin da suke ciki a matsayin gaba kura baya sayaki.
Na dora wannan ra’ayi nawa kan dalilai kamar haka; Idan aka yi sulhu aka biya bukatun gwamnoni, wanda nake zaton haka za ta faru, duk da ba a yin bari a kwashe daidai, za a samu daidaita ne sakamakon manyan PDP kuma iyayen gidan wadannan G-7 wato Obasanjo da Janar Babangida ba su son a lalata PDP a kashe ta murus.
Da zarar an yi haka ga abin da zai biyo baya: girman G-7 zai fadi kuma za a kulla gaba ta sirri a tsakanin mutanen bangaren Shugaban kasa da na gwamnonin kuma kowa zai ci gaba da cin dunduniyar dan uwansa domin samun biyan bukatar siyasa. Na biyu; ba za a samu zaman lafiya ba na siyasa ta cikin gida a jihohin G-7, saboda masu murna an rabu da kaya murnarsu za ta koma ciki kuma za a ci gaba da samun sabani ko a wani lokacin ma rigima.
Wani abu kuma wanda shi ne na uku, ba lallai ba ne kuma idan ’yan G-7 sun zo da wata bukata tasu ko ta mutanensu ko ta siyasa ko aikin gwamnati, kamar takara da nade-naden mukamai, nan take su samu biyanta daga bangaren Shugaban kasa. Su kuwa talakawa za su ce shi ke nan da ma can wasa ake yi da hankalinsu karya ce ba domin kishin Najeriya ko kwato ’yancin talaka ake wannan hayaniya ba, domin son zuciya ne, su kuma sai a rasa goyon bayansu da addu’o’insu.
Amma kuma idan ba a samu sulhu ba, abin da G-7 za su hadu da shi yana da yawa. Na daya: duk wata bukatarsu ta kasa ta sha ke nan sun koma abokan gaba sun zama makiya. Na biyu Gwamnatin Tarayya za ta yi amfani da duk irin karfin ikon da take ta shi ta fuskar tsaro da kudi da shari’a da mulki ta cusguna wa ’yan G-7, a nan kuma za a duba kowace jiha ce a daukar mata mataki daidai irin nata.
A jihohin da G-7 suka karbi APC ko wata jam’iyya za a samu talakawa su dan tausaya musu, su yi musu marhabin lale, idan suka tada kurar kabilancin yanki da kabilancin addini, amma kuma PDP za ta kara rura wutar rikicin cikin gida na magoya bayan tsofaffin ’yan APC da G-7, wanda zai hana zaman lafiya a duk jam’iyyar da suka shiga, kuma tun da bukatar maje Hajji Sallah, duk dan siyasa yana son cin zabe ne, sai a zo a yi uwar watsi.
Gaskiyar magana da na sha fada wannan rikicin da G-7 suka tsiro da shi ba shi da wata rana balle amfani. Yin sa cutar da talakawa ne da raba kansu. Idan har G-7 sun hakkake karbar mulki suke son yi, kwanton bauna ya kamata su yi tun farko su yi namijin shiri, su biyo ta bayan gida ba wai su fito fili kowa ya gansu ba. Yanzu an san alkibarsu kuma za a shirya wa duk wani taku nasu a doke shi, a hana masa kai labari.
Ya kamata mu sani cewa lokaci ya yi da za mu ajiye neman biyan bukatunmu na siyasa daga masu mulki ta hanyar rudu da hayaniya. Babbar hanya ita ce ta kyakkyawan shiri da fitar da ingantacciyar manufa. Babu wanda zai ji dadi idan yau G-7 sun fita sun kafa ko sun shiga wata jam’iyya, sannan sun yi duk bakin koakrin ganin hakansu ta cimma ruwa, amma duk da haka Jonathan ya samu dama ya ci gaba da irin wannan mulki maras dadi a 2015 zuwa 2019, ai an kai ‘yan Najeriya an baro su, kuma ba laifin kowa sai wadannan ’yan G-7 da kuma sauran ’yan siyasar da suka gaza gano haka a cikin ’yan adawa.
G-7 sun saka kansu da kansu cikin tsaka mai wuya, idan ba wata kudura ta Allah ba, mu ma mabiya za su sanya mu cikin wahalar. Allah Ya sa mu dace.
Amma wannan duk hasashe ne, saura duk na Allah ne domin Shi ne Masani.

Bello Muhammad Sharada
ya rubuto ne daga Kano
za a iya samunsa a
[email protected]
ko 08059165260

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno