Wa ya tsine wa Najeriya? (1)

Lokacin da muke yara kanana a kauye, ba abin da muka fi jin haushi irin tsinuwa, ko cikin wasa ba a son a ce wani (abokan wasa, tsofaffi da makamantansu) sun tsine ma ko sun nemi a tsine ma ko kuwa iyaye su kama zancen tsinuwa a bakinsu dangane da abin da suka haifa. Tsinuwa […]

Wa ya tsine wa Najeriya? (1)
Wa ya tsine wa Najeriya? (1)

Lokacin da muke yara kanana a kauye, ba abin da muka fi jin haushi irin tsinuwa, ko cikin wasa ba a son a ce wani (abokan wasa, tsofaffi da makamantansu) sun tsine ma ko sun nemi a tsine ma ko kuwa iyaye su kama zancen tsinuwa a bakinsu dangane da abin da suka haifa. Tsinuwa kowace iri ce, bala’i ce, shi ya sa ko tsakanin tsararraki a filin wasa ko kwallo, idan ka yi laifi aka ce ka yi, ka musa, to karyar nan na iya jawo maka tsinuwa, amma ko a lokacin ba a jefa tsinuwar kai tsaye, sai an yi wasa da ita. Saboda haka ba abin mamaki ba ne a ji yara na cewa, ‘Allah tsinini, Allah tsine, Allah tsine uwar mai karya;’ wani kafin ma a ida za ka ji yana cewa don Allah a bari, ku ba ku san wasa ba. Ba fa shi za a tsinewa ba, ‘uwar mai karya’ aka ce, amma kowa ya san tsinuwar da ta bi uwa, na iya bin har ’ya’yanta, saboda haka kada a fara.
Ke nan tun a wancan lokaci tsinuwa ko a tsine wa mutum, babbar magana ce. Tsinuwa bala’i ce. Tsine wa yaro ko daga bakin yaro dan uwansa abin ki ne, domin kuwa ba yaran ne ke yin tsinuwar ba, Allah ne ke tsinewa, duk kuma wanda Allah Ya tsine wa, ya shiga uku, ya balbalce. Idan kuwa tsinuwar daga bakin iyaye ta fito, ita ma ba ta da dadi, domin kuwa tofin Allah-tsine na iyaye ya fi komai zafi a cikin al’ummar wancan zamani. Dukkan wadannan lamurra na tsinuwa suna zuwa bisa tawassuli da Allah, amma tsinuwar iyaye ta fi komai saurin karbuwa saboda kusancin da da iyayensa.
Wannan ne ya sa a wancan lokaci, duk ’ya’yan da iyaye da suka tsine mawa za a ga ba sa albarka, ba sa gudanar da rayuwarsu yadda ya kamata. Idan har sun rayu, to za a same su ko dai sun zama gawurtattun ’yan iska, su ne yawo kwararo-kwararo ba sana’ar hannu, balle su tabuka komai a rayuwa. Su ne a gidajen karuwai ko zauna-gari-banza, ba su da aikin fari, balle na baki. ’Ya’yan da iyaye suka tsine mawa ko rigar kwarai ba a ganinsu da ita, kullum cikin tsumma ko ragga, idan tsinuwar ta kai karo kuwa, to sai hauka. Shi ya sa duk lokacin da muka ga mahaukaci na ta gararamba a titi, ga shi da iyaye da ’yan uwa, ba wanda ya damu da shi, ba abin da ke zuwa a rayuwarmu, sai kila wannan yaro ko yarinya, ya saba wa iyayensa ne, shi ya sa suka tsine masa, ga shi ya haukace. Domin a tunaninmu na wancan lokaci, hauka shi ne karshen tsinuwar iyaye ga ’ya’yansu.
kila zuwa yanzu mai karatu ya fara tambayar kansa, me ya hada batun tsinuwa da Najeriya? Sai na ga kila tambayar ba ta da wuyar amsawa idan muka dubi halin da kasarmu Najeriya take ciki a halin yanzu, ko kuma daga ’yan shekarun da ba su kasa 15 da suka wuce ba. Idan na tsaya tsaf sai na ga kamar Najeriya ta yi wa iyayenta laifi ne, irin wanda ’ya’ya ke yi wa iyaye har aka yi mata tofin Allah-tsine, ta lalace, ta balbalce, ta shiga duniya tana yawon hauka. Me ya sa na ce haka?
Mu kididdige yadda rayuwar Najeriya take ciki a halin yanzu mu ga idan ba alamun tsinuwa tare da Najeriya.
• A da ko in ce cikin shekara 50 da suka wuce, Najeriya kasa ce mai arziki da wadata, kowa na ji da ita a fagen tattalin arziki, komai game da rayuwar al’ummarta ta fuskar inganta tattalin arziki na gudana yadda ya kamata. Amma me ya faru cikin wannan tsawon shekaru, arzikin Najeriya ya watse, kasar ta talauce, duk wani ci gaba nata ya durkushe, ta yadda yanzu ba a yi mata komai sai dariya, saboda arzikin da take takama da shi yanzu babu. Talauci ya cika kasa ta yadda ciyar da kanta da ’ya’yanta ya zame mata matsala. Mene ne wannan in ba alamun tsinuwa ba?
•  A cikin wadannan shekaru da muke magana Najeriya ta shiga cikin taskun rayuwa ta fuskar gudanar da mulki, shugabanninta, wato wasu daga cikin ’ya’yanta, sun kasance Fir’aunonin zamani, sun haye kanta sai sukuwa suke, kowa sai kuka da tsuwa yake saboda mugun mulkin ’ya’yanta. Ita kuka, sauran al’ummarta ihu. Wasu daga cikin ’ya’yan nata (masu mulkin, soja da farar hula) sun bi sai sukuwa suke a cikin kasar, sun danne, sun murkushe, sun daure, sun shakure, sun harbe, sun kashe, ba kuma abin da wani zai iya yi, mene ne wannan in ba alamun an tsine wa kasar ba, ta yadda ’ya’yanta da jikoki sun tarwatse, sun lalace, ba su iya agazawa ko taimaka wa mahaifiyarsu?
• Ba wannan ba kadai, ka dubi irin tarin dukiyar da a da Najeriya ke da ita, amma da yake bakin iyaye ya bi ta, me ya faru, ta tsiyace, ta talauce, ta sangarce. Dubi irin hanyoyin samun da ke tattare da ita a can da, noma, kiwo da sana’o’in hannu bilahaddin, amma yanzu fa, saboda tsinuwa ta yi watsi da komai da komai ta kama saba-likita, sabuwar sana’ar da ta kama ta sayar da mai, nan ma tsinuwar ba ta bar ta, domin komai ta taba dangane da harkar sayar da man, sai ka ga ya sukurkuce, ta kama hanyar shiga tasku, ko ma ta yi gida ta zaune a ciki. Yanzu man fetur da Najeriya ke sayarwa ya zame mata ciwon sankara, ga arziki, amma arzikin banza, saboda lalacewa da shirmancewa idan ta sana’anta man fetur din ma, ta samu dukiya mai yawa, ba wani amfani da dukiyar ko arzikin na man fetur ke yi mata ko ’ya’yanta, shin mene ne wannan in ba alamun tsinewa ba?
• Wani abin kara la’akari da rayuwar Najeriya dangane da tsinuwa shi ne, irin yadda komai na gidan nata ya lalace. Abincin da za ta ciyar da ’ya’yanta ya gagare ta. Ilimin da za ta ba ’ya’yan nata, ya faskara. Hanyoyin da ake bi a cikinta sun kasance godabun wahala, ka bi da mota, ta lalace, ka hau su da babur, ka sha wahala, ka bi su da keke, gare-garen ya malkwade, ka taka a kasa ka yi ta fama da tuntube da gulando. Hanyoyin dogo ko jirgin kasa duk sun lalace, jiragen sama tuni sun yi hijira daga kasar, duk wata hanyar zirga-zirga a cikin Najeriya ta gani da fada ba daya da za a ce na aiki; ina marabin wannan da wanda aka tsinewa a cikin rayuwa?
• Haka kuma saboda tsinuwa na bin ’ya’ya, wata sa’a ma har da zuwa ga ’ya’ya da jikoki da alama tsine wa Najeriya da aka yi ya shafi har ’ya’yanta. Kashi saba’in cikin dari na ’ya’yan nata ba su iya ciyar da kansu, talauci ya yi musu katutu. Rabin ’ya’yan nata kuma ba su da aikin yi, masu dukiya daga cikin ’ya’yan an hana musu godiya, marasa dukiyar kuma an hana musu dangana. Ba ka jin komai daga ’ya’ya Najeriya sai Allah wadai da kukan dimuwa da damuwa. Duk wannan mene ne in ba siffofin tsinuwa ba?
Idan mutum ya ce zai tsaya ya lissafe alamun da ke nuni ga cewa an tsine wa kasarmu Najeriya, to, sai ya cika littattafai, domin kuwa ga su nan ba sa kirguwa. To amma koda muke rayuwa irin ta yara a wancan lokaci, abin da mutumen da aka tsine mawa ke yi shi ne su gane wanda ya tsine musu domin su nemi gafara, don a sake sabuwar rayuwa. Tambayar da nake wa kaina dangane da Najeriya shi ne, ita wa ya tsine mata? Wa ta yi wa laifi har baki ya shafe ta? Wa za ta nemi afuwa wurinsu domin a yafe mata, a yaye rigar tsinuwar, domin ta koma yin rayuwar da ta dace da ita? Shin iyayen Najeriya ne suka tsine mata ta lalace haka, har abin ya shafe mu, ’ya’ya da jikoki? Ko kuwa wani tsoho ne daga cikin al’ummar Najeriya ta yi wa rashin kunya, har ya buda baki ya ce, je ki, kya gani? Ko kuwa dai ita Najeriyar ce ta tsine wa kanta da kanta, domin ta sa ’ya’yanta cikin tasku da gagari, ganin cewa ’ya’yan nata ba na kwarai ba ne, wato su kasance cikin tasku da tashin hankali, saboda rashin tarbiyya da ladabi da biyayya? Ko kuwa dai ita Najeriyar ce da kanta ta tsine wa ’ya’yan nata domin su lalace?
 
Za mu ci gaba