Wa yake murna da sojojin taron dangi a Najeriya?

Daga Jibril Abdul Daura Gwamnatin Najeriya ta nemi dauki daga manyan kasashen duniya da su taimaka mata domin kawo karshen rikicin ‘yan kungiyar tayar da kayar baya ta Boko Haram. Agajin da za a bayar ga Najeriya sun hada da sojoji da ‘yan sanda da kwararru a fannin tattara bayanai da bincike da karbar mutanen […]

Wa yake murna da sojojin taron dangi a Najeriya?
Wa yake murna da sojojin taron dangi a Najeriya?

Daga Jibril Abdul Daura

Gwamnatin Najeriya ta nemi dauki daga manyan kasashen duniya da su taimaka mata domin kawo karshen rikicin ‘yan kungiyar tayar da kayar baya ta Boko Haram. Agajin da za a bayar ga Najeriya sun hada da sojoji da ‘yan sanda da kwararru a fannin tattara bayanai da bincike da karbar mutanen da aka yi garkuwa da su, kai da ma duk wasu masana a fannonin harkar tsaro. Tare da na’urori na zamani da kuma sauran kayan aiki da suka shafi samar da tsaro. Wa yake murna da sojojin taron dangi a Najeriya?
Wannan taimako da mahukunta Najeriya suka nema daga kasashen Turai ya tabbatar da gazawar gwamnati wurin magance rikicin ‘yan kungiyar Boko Haram. Kamar yadda wani soja daga rundunar sojojin Najeriya ya fada da kuma furucin Gwamnan Barno Kashim Shatima cewa gwamnati ta kasa
samar da jami’an tsaro da makamai da kayan aikin da za su iya tunkarar ‘yan Boko Haram.
Shi dai yankin Arewa maso Gabas ya fada cikin rikicin ‘yan kungiyar Boko Haram ne kimanin shekaru biyar da suka gabata. Tashe-tashen hankulan sun janyo asarar rayukan dubban mutanen da ba su ji, ba su gani ba, da kuma asarar dukiyar bayin Allah mai tarin yawa. Al’ummomin yankin na cikin tsanin tsoro da fargaba sakamokon tabarbarewar al’amuran yau da kullum. Harkoki sun tsaya cak, kashe-kashen mutane sun yawaita da hare haren kunar bakin wake da kisan kai na kare dangi. Ga cinna wuta da ake yi a gidajen jama’a da kone makarantu, sannan kuma ga annobar sace mutane da garkuwa da ake yi da su. Kamar abin da ya faru a Cibok, wadannan matsaloli sun tagayyaira mazauna yankunan, tare da dimautasu. Yayin da kuma dubun dubatar jama’a suka tsere wa gidajensu da garuruwansu domin tsira da rayukansu.
A halin yanzu mutanen yankunan suna tsananin dokin ganin an kawo karshen wannan balahirar da ta daidaita su da kuma fatan ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali sun dawo.
Mu ba wai muna adawa da shigowar sojojin kasahen waje ba ne. A’a, abin da shigowar tasu ka iya haifar shi ne abin ji!
Da farko akwai ka’idoji da kuma sharudda da suke gindiyawa kafin fara aiwatar da ayyukansu, ga kuma zunzurutun makudan kudi da ake ware masu domin bukatunsu. Sannan suna da damar shiga duk gidan da suke so, kuma a lokacin da suka so, ba tare da wani shamaki ba. Wanda hakan ya saba wa koyarwar addinanmu da kuma al’adarmu. A baya mun ga abin da ya faru a kasashe da dama a sassan duniya sanadiyar mamayar sojojin
Amurka da na taron dangi da zummar zuwa kwantar da tarzoma ko yaki da ta’addanci. Sannan mun ga abin da ya biyo baya wanda bai haifar da da mai ido ba. Kamar mamayar da Amurka ta yi a Somalia, bayan hambarar da Gwamnatin Saed Bare, har ya zuwa yau sama da shekaru 20 ke nan, amma an kasa samun dauwamanmen zaman lafiya da gwamnati mai karfin iko a duk fadin kasar.
Haka a Afghanistan da Irak kusan kullum hare-haren kunar bakin wake da rikicin addini a tsakanin mabiya mazahabobi daban-daban da suke ta kashe junansu bayan fitar Amurka da kawayenta. A Libiya tun bayan da aka kifar da Gwamnatin Gaddafi da Yammacin duniya suka yi sun tafi sun bar kasar cikin tsananin rigingimu da rikicin cikin gida, ga tattalin arzikinsu ya karye an kasa samun zaman lafiya. A yanzu kusan shekaru hudu ke nan, amma Firayiminista na biyar za a zaba a wannan dan lokacin.
Soboda haka ya kamata mahukuntan Najeriya su yi tunani mai zurfi, tare da daukar darasi ga abin da ya faru a wasu kasashen kafin yanke wannan danyen hukuncin. Tarihi ba zai taba mantawa da muhimmiyar rawar da jami’an tsaron mu suke bayarawa wajen kwantar da tarzoma a kasashen Afirka ba. Kamar a Kongo da  Liberiya da Saliyo da Mali da sauransu. Duniya ta shaida hazakar su, tare basirar sanin makamar aiki. Amma an ce sun gaza har sai an gayyato masu jan kunne, me zai hana gwamnati ta tuntubi tsofaffin jami’an tsaronmu, domin samun shawarwari da dubarun da za a bi, domin kawo karshen wannan masifar, maimakon gayyato kasashen Turai?
Muna da tsofaffin shugabanin kasa soji, har guda biyar masu rai, wanda kowane daga cikinsu ya yi gwagwarmaya akan sha’anin tsaro, suna da gogewa da kwarewa a kan tsaro, kowa ya kai matakin babban janar na soja. To a tuntubesu mana, domin samun shawarwari da hanyoyin da ya kamata a bi domin ganin karshen wannan masifa idan har gwamnati da gaske take.
A yanzu dai ta riga ta faru ta kare, sojojin Amurka sun riga sun fara shigowa kasar nan. Fatanmu Allah Ya sa su tsaya kan abin da ya kawo su, su gama lafiya su bar mana kasarmu cikin aminci, Amin.
Injiniya Jibril Abdul Daura 08038997861, 08022997340.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya