Wa yake son kashe Buhari?

A yanzu dai ta tabbata cewa, babu shakka wani yana son ganin gawar Janar Muhammadu Buhari. Bai dace a dauki abin da ya afku a ranar 23 ga Yuli, 2014 da wasa ba. Idan da a ce muna da gwamnati ta gari, da yanzu ta dauki matakin bincikawa da bankado badakalar da muhimmancin gaske. Janar […]

Wa yake son kashe Buhari?
Wa yake son kashe Buhari?

A yanzu dai ta tabbata cewa, babu shakka wani yana son ganin gawar Janar Muhammadu Buhari. Bai dace a dauki abin da ya afku a ranar 23 ga Yuli, 2014 da wasa ba. Idan da a ce muna da gwamnati ta gari, da yanzu ta dauki matakin bincikawa da bankado badakalar da muhimmancin gaske. Janar Buhari ba karabitin dan Najeriya ba ne. Tsohon shugaban kasa ne, kuma jagoran jam’iyyar adawa ne a kasar nan.
Shi kan shi Buhari ya gaskata cewa kisan gilla a kayi yunkurin aikata masa, amma gwamnati da ’yan kanzaginta sun ce, idan har kashe shi a ka yi niyyar yi, to ya binciki cikin jam’iyyarsa ta APC. Wasu ma har sun wuce gona da iri su na zargin sauran ’yan takarar shugaban kasar da ke cikin jam’iyyar. Sai dai lamarin ma ya wuce nan, inda Mujahid Dokubo-Asari ya ce, Buharin ne da kansa ya kulla kai wa kansa harin, domin kawai ya bata wa maigidansa, Goodluck Jonathan, suna. Ban san wannan mutum ya na da hazaka haka ba. Dakiki kawai! Masu yi wa Buhari fatan alheri na ganin cewa, na kusa da Jonathan ne ke son ganin bayanshi,sabanin yadda ake kokarin daukar alhakin ‘’yan adawa na Jam’iyyar APC..
Awanni kafin kai harin, Buhari ya ce Jonathan ya kaddamar da yaki a kan ’yan Najeriya, inda hakan ya haifar da martanin da ke nuna kamar abin da Buharin ya fada ya tabbata. Babu wanda ya fito kai tsaye ya zargi Jonathan da yunkurin kashe Buhari – akalla ban ji hakan a bainar jama’a ba, amma sai dai akwai wasu hujjoji masu wuyar warwarewa. Ba dole ne mutum ya so tsohon shugaban kasa Obasanjo ba, kuma ni ba na tare da shi – amma ba za ka dauki maganar da ya fada a kan wannan gwamnati da wasa ba. Shin ba shi ne ya dasa gwamnatocin Jonathan da Yar’aduwa ba ne? A cikin wata muhimmiyar wasika da ya aike wa Jonathan, Obasanjo ya bayyana cewa ya na sane wasu ’yan bindiga da a ke bai wa horo domin su yi wa Shugaba Jonathan aiki a zaben 2015 da ke tafe.
Don Allah kada wanda ya ce mini wai kada na dauki maganar nan ta Obasanjo da wasa. Idan har akwai mutane dubu (1,000) a jerin sunayen wadanda za a bindige, kamar yadda Obasanjo ya yi ikirari, to fa kuwa ya san abu ne mai yiwuwa sunan Buhari ya zamo a na farko-farko. Hakan na iya faruwa. Ta yiwu wadanda a ka dauki nauyin su aikata kisan sun fusata da kalaman na Buhari ne kan gwamnati. Don haka suka yanke shawarar fara daukar mataki nan take.
Zai iya yiwuwa kuma Boko Haram ne ke son kashe Buhari, saboda irin harin da aka kai Kaduna a ranar ya yi kama da na Boko Haram, harin zai iya yiwuwa an shirya shi ne tare da na Sheikh Dahiru Usman Bauchi, malamin darikar Tijjaniya. Shin Boko Haram suna son kashe Buhari ne don yana kalubalantar ayyukan su ko kuwa? Idan haka ne, to ya fito fili ke nan, masu alakanta Buhari da daukar nauyin Boko Haram sai su je su nemo wanda yake daukar nauyin kungiyar ba Buhari ba, idan har suna son kashe Buhari, to lallai ba abokinsu ba ne ke nan.
Sakataren yada labaran PDP, Mista Olisa Metuh, ya ce yunkurin kashe Buhari a zargi abokan takararsa na APC. Ban san ko hakan zai zama abin dubawa ba. Shin idan har wani a cikin APC yana son kashe Buhari sai ya yi amfani da kunar bakin wake? Ko ma dai mene ne, ko Boko Haram ne ke son kashe Buhari ko mutanen PDP, ko kuma abokan takararsa a APC, hakan na faruwa ne karkashin Gwamnatin Jonathan, wanda kuma ya zama dole ta kare rayukan jama’arta, ko da kuwa a cikin APC ne ake son kashe Buhari, ya zama dole gwamnati ta kare lafiyarsa, yadda kusoshin PDP ke magana kan harin, ya nuna cewa ko kadan ba su san takamaimai nauyin da ya rataya a wuyan su ba.
Shin me ya sa har yanzu gwamnati ta kasa gano masu daukar nauyin Boko Haram? Shin mutane za su yarda cewa Gwamnatin Jonathan ba ta san masu bai wa ‘yan ta’adda makamai ba?
An ya kuwa akwai wanda zai yarda da hakan? Idan haka ne me ya sa har yanzu suke kan karagar mulki? Akwai tambayoyi masu yawan gaske da suke bukatar amsoshi. Abin dai kullum yana kara tabarbarewa ne, lokaci ya yi da Najeriya take bukatar samun shugaban da ya cancanta. A yanzu kam ba mu da shi. Yanayin kullum sai kara zama abin tsoro yake yi, tunda a ranar talata 8/1/2013, ministan watsa labaran Najeriya, Mista Labaran Maku, a Radiyon Faransa da safe ya ce, Gwamnatin tarayya ta ware biliyoyin Naira domin ayyukan raya kasa a Arewacin Najeriya, amma rashin tsaro da ya addabi jahohin Arewa ya sa ba za a iya yi ba. Abin tambaya a nan shi ne, alhakin tsaro a wuyan wa yake?
Sauran bangarorin Najeriya da ake satar mutane: baki da ‘yan kasa har da mahaifiyar Ministar kudi, suna da cikakken tsaro da aka nunnuka musu kudinmu? Hakkin kowace gwamnati ce ta samar da tsaron rayuka da lafiya da dukiya da mutunci da addini ga kowa da kowa, ‘yan kasa da baki. Duk abin da ya gaza cikin biyar din nan, gara a san babu wannan gwamnati, kowa ya nemi abokan zaman tare, su rika kare kansu da kansu. ‘Yan uwa kun ji fa yadda ake yin kantafi-mafarin asara da rayuka da dukiyarmu gwamnatin tarayya ta hana ‘yan arewa hakkinsu da sunan rashin tsaro, bacin ita ke da alhakin samar da tsaro ga kowane bangare.

Anas Saminu, Ja’en Makera, Jami’in Hulda da Jama’a  a kungiyar Muryar Talaka, Reshen Jihar Kano. 07033882307,08188742103.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya