Wa za a dora wa alhakin yawan faduwar dalibai jarabawar NECO da WEAC?

Tuni dai daliban gaba da firamare suka fara rubuta jarabawar karshe (WEAC da NECO), kuma ana ta kuka da yadda musamman a jihohin Arewa daliban ke yawan faduwa, inda da kyar ake samun kalilan da suke samun nasarar samun darajar cancantar shiga jami’a. Abin tambaya a nan shi ne, shin wa za a dora wa […]

Wa za a dora wa alhakin yawan faduwar dalibai jarabawar NECO da WEAC?
Wa za a dora wa alhakin yawan faduwar dalibai jarabawar NECO da WEAC?

Tuni dai daliban gaba da firamare suka fara rubuta jarabawar karshe (WEAC da NECO), kuma ana ta kuka da yadda musamman a jihohin Arewa daliban ke yawan faduwa, inda da kyar ake samun kalilan da suke samun nasarar samun darajar cancantar shiga jami’a. Abin tambaya a nan shi ne, shin wa za a dora wa laifin, daliban ne, malaman ne, hukumomin jarabawar ne ko kuwa gwamnati? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga abin da suke cewa:

Laifin hukumomin ilimi ne – Hauwa’u Adamu

A.A. Masagala, a Benin

Hajiya Hauwa’u Adamu Kawu: “A gaskiya wannan lamarin matsalar hukumar ilimi ce ta kasa, ita ce ba ta tafiyar da harkar makarantun kasar nan bisa ka’ida da tsari na kwarai; har ya kai idan dalibanmu suka rubuta jarabawa sai ka gani ana zubar da su da dama kuma ba don komai ba illa sakaci da yin ko oho daga hukumar ilimin ta kasa. Dalilina na farko shi ne, idan muka yi la’akari da irin littatafan da ake koyarwa, ba na zamani ba ne, tsofaffin littattafai ne da aka daina yayinsu ko amfani da su. Maimakon a samar da abin da zamani yake tafiya da shi bai daya a tsarin na littattafan koyarwar amma ina? Kowace jihar nata daban, wannan ya sa idan aka duba akwai bambanci a irin wadannan littattafan da mafi yayawan makarantu na kasar nan suke anfani da su wajen koyarwa kuma akwai mu da makarantu masu zaman kansu, su ma wasu littatttafansu sun sha bamban da ainihin na gwamnati. Saboda haka ina ganin abu ne mai wuyar gaske hukumar shirya jarabawa ta kasa ta iya tantance tare da tsara jarabawa da mafi yawan dalibai ba za su fadi ba; ga kuma uwa uba rashin kyautata wa malaman wajen biyansu hakkokinsu na koyarwa.”

Malaman makaranta ke da laifi – Aliyu Abubakar

A.A. Masagala, a Benin

Aliyu Abubakar: “Ra’ayina da fahimtata, kowane bangare na hukuma mai kula da sha’anin ilimi da makarantu a kasar nan suna da irin gudunmowar da suke bayarwa don taimaka wa faduwar dalibai a jarabawa  amma babbar matsalar tana daga wajen malamai masu koyarwa a makarantun kasar nan. Dalilina shi ne, ganin yadda mafiya yawa daga cikin malaman ba su son tsayawa suna koyarwa kamar yadda ya dace; kawai suna zuwa ne su zauna cikon lokaci. Wani kuma a mako ba ya wuce ya zo sau daya rak, wasu kuma idan ka gansu lokacin karbar kudin wata ne ya yi, don haka zuwan ba don Allah ba ne, balle su shiga aji su koyar. Kuma wani abin takaici, idan har aka zo dab da lokacin jarabawar ta karshe, ba su yi wa daliban bita yadda za su iya fahimtar wani abin da zai taimake su na cikin jarrabawa kuma sai a kurarren lokaci wanda yin haka ina ganin yana kawo matsala ga dalibai masu rubuta jarabawa; domin tun da farko malaman sun ki su tsaya su koyar da daliban yadda ya kamata. Don haka irin wadannan matsalolin suna nan da dama daga kowane bangare kamar yadda na fara fada tun da farko.”

Laifin Gwamnati ne – Musa Cairo

Lubabatu I. Garba, a Kano

Alhaji Musa Cairo Yakasai: “A ra’ayina, laifin na gwamnati ne gaba daya. Faduwar jarrabawa tana samuwa ne sakamakon halin fatara da talauci da muutanen kasar nan suka tsinci kansu a ciki. Malamai da dalibai dukkkaninsu ba sa cikin natsuwar da za su iya yin abin da ya kamata su yi. Malami yana tunanin abin da zai ci, ba zai iya tsayawa ya koya wa dalibai abin da ya kamata su sani ba. Shi ma dalibi a nasa banagaren yana cikin yunwa, don haka ba zai iya fahimtar abin da malamai ke koya masa ba.”

Gwamnati za a dora wa laifi – Adamu Azare

Sani Gazas Chinade, a Damaturu

Malam Adamu Azare: “A ganina yawaitar faduwar jarabawa da daliban makarantun sakandare ke yi a jarabawar kammala makaranta ba laifin kowa ba ne in ba na gwamnati ba. Dalilina na fadar haka kuwa shi ne, ai ita gwamnatin a mafi yawan jihohin kasar nan, musamman ma a Arewa, su ne ke biya wa dalibai kudaden rubuta jarabawar NECO, WAEC, NAPTEB da makamantansu, to me zai hana gwamnatin ta rika tsawatarwa ga hukumomin shirya jarabawar, don rage yawaitar kada daliban. Haka kuma ta rika tsawatar da daliban da su rika karatu. Don haka akwai bukatar Gwamnatin Tarayya ta rika tsawatar wa dukkan bangarori don rage yawaitar faduwar daliban da ake samu. Idan ta yi hakan to akwai yiwuwar kwalliya ta iya biyan kudin sabulu.”

Laifin dalibai da gwamnati ne – Nura Uruma

Lubabatu I. Garba, a Kano

Nura Uruma kofar Mata: “Laifin na dalibai ne domin dalibai ba su mayar da hankali kan abin da ake koya musu. Yawancin dalibai idan suka koma gida ba su bitar abin da aka koya musu. Sai ka ga idan jarrabawa ta zo ba su iya amsa tambayoyin da aka yi musu. Laifin gwamnati a nan shi ne, ba ta kula da hakkin malamai. An bar malamai babu cikakken albashi, babu karin girma, sai ka ga shi ma malamin hankalinsa ya rabu biyu, yana can yana yawon neman kudi a hannu guda kuma yana koyarwa.”

Laifin na Gwamnati ne sosai – Ahmad Modu

Sani Gazas Chinade, a Damaturu

Ahmad Alhaji Modu: “A ganina, yawaitar faduwar jarabawar karshe da daliban makarantun sakandare ke yi, laifin gwamnati ne matuka. Dalilina na ambata haka kuwa shi ne, ai idan da gwamnatin ta ga dama da za ta iya daukar matakin tilasta wa malamai su yi aiki bil-hakki da gaskiya tare da jan kunnen dalibai da su yi karatu kana gwamnatin ta kuma gargadi hukumomin shirya jarawaba, da su rage matse hannun da suke yi don ba da dama ga daliban, iliminsu ya inganta. Don haka in dai ana son rage yawaitar faduwar da dalibai ke yi a jarabawarsu, to ya zama wajibi gwamnati ta dau matakin ba-sani-ba-sabo tun da kai da kaya duk mallakar wuya ne.”